Hukumar Tsaro da Kare Muhalli ta Kasa (NSCDC), Jihar Jigawa, ta bayyana bakin cikinta tare da la’antar kisan wulakanci da aka yi wa wata yarinya ‘yar shekara uku mai suna Harira Yakubu Bala, mazauniyar unguwar Sabon Gari, karamar hukumar Kiyawa. An gano gawarta a cikin daji da safiyar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025.
Rahotannin farko sun nuna cewa iyayenta sun bayyana rashin ganinta da misalin karfe 11:00 na safiyar Talata, 14 ga Oktoba, 2025. Abin takaici, cikin sa’o’i 24 kacal, an gano gawarta cike da raunuka da alamun cin zarafi da kisa cikin zalunci.
Bayan samun kiran gaggawa, jami’an NSCDC daga ofishin Kiyawa karkashin jagorancin Superintendent of Corps (SC) Shamsuddeen Amin suka garzaya wajen, suka kebe yankin tare da kwashe gawar don bincike da gwajin likita.
Binciken likitanci ya tabbatar da cewa an yi wa yarinyar fyade kafin a kashe ta cikin zalunci, wanda har yanzu ba a kama wadanda suka aikata wannan ta’asa ba. Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin mugunta, rashin imani da cin zarafin dan Adam wanda ya sabawa duk wani ka’idar ɗabi’a da addini.
Shugaban Hukumar NSCDC na Jihar Jigawa, Commandant Muhammad Kabiru Ingawa, ya bayar da umarni ga sashen leken asiri da bincike na hukumar da su hada kai da ofishin Kiyawa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata laifin, kuma an gurfanar da su a gaban kuliya.
A halin yanzu, an mika gawar marigayiyar ga iyalanta domin yi mata jana’iza bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Commandant Ingawa ya mika sakon ta’aziyya ga





