Wata kungiya ta kakakin hulda da jama’a daga hukumomin tsaro da paramilitari daban-daban ta kai ziyarar ban girma ga Babban Kwamandan Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (FFS), Olumode Samuel Adeyemi, a ofishin hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Juma’a.
Ziyarar, wadda Mataimakin Kwamandan Gyaran Hali Abubakar Umar, mai magana da yawun Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa ya jagoranta, ta yi nufin ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi, gina ɗaya gari, da kuma samar da tsari guda wajen sadarwa da jama’a don amfanin tsaron ƙasa da kare lafiyar al’umma. Tare da shi a ziyarar akwai Laftanar Kanar O. A. Anele, mai rikon mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja, da Babban Sufeto Babawale Afolabi, mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC).
Da yake maraba da tawagar, Babban Kwamandan ya yaba da wannan ƙuduri tare da jaddada cewa ingantacciyar sadarwa da haɗin kai tsakanin hukumomi muhimman kayan aiki ne wajen gina amincewar jama’a da tabbatar da tsaron ƙasa baki ɗaya.




