Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC), Farfesa Ahmad Abubakar Audi, mni, ya yaba wa Hukumar Kiyaye Hadurran Hanya ta Tarayya (FRSC) bisa yadda ta ci gaba da aiwatar da ingantaccen Tsarin Auna Ayyuka da Inganci (Performance and Quality Management System) tsawon shekaru 16 ba tare da tangarda ba, yana mai bayyana tsarin a matsayin abin koyi ga sauran hukumomi.
Farfesa Audi ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Babban Kwamandan FRSC, Shehu Mohammed, mni, inda ya jinjina wa hukumar kan daidaito, tsari, da kwarewa da ke tattare da tsarin gudanarwarta. Ya ce tsarin FRSC ya dace da ka’idojin kasa da kasa na auna aiki da ingancin gudanarwa, kuma hakan ya taimaka matuka wajen inganta hidimar jama’a.
A cewarsa, ziyarar ta zo ne bisa umarnin Shugaban Kasa wanda ya umurci hukumomin gwamnati da su yi nazari kan tsare-tsare da tsarin aiki da suka tabbatar da inganci, gaskiya, da daukar alhaki a hidimar jama’a.
Babban Kwamandan NSCDC ya tabbatar da kudurin hukumar na yin cikakken nazari kan dukkan bangarorin Tsarin Auna Ayyuka na FRSC, da nufin daukar darussan da suka dace domin karfafa hanyoyin aiki na cikin gida da inganta tasirin ayyukan hukumar.
Ya kara da cewa irin wannan hadin gwiwa tsakanin hukumomi zai taimaka wajen kara bin ka’idojin inganci a fadin NSCDC, tare da inganta hidimar tsaro da kuma kara amincewar jama’a ga hukumomin tsaro na kasa.




