Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (FFS) a ranar Alhamis ta gaggauta mayar da martani bayan samun kiran gaggawa daga wani mai gari game da gobara da ta tashi a wani gini mai bene biyu da ke wajen kasuwanci a Utako, Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da jami’an kashe gobara suka isa wurin, sun tarar da ginin yana cike da harshen wuta, nan take kuma suka kaddamar da aikin kashe gobara cikin tsari da haɗin kai, wanda ya kai ga kashe wutar cikin ɗan gajeren lokaci.
Mutane maza shida masu shekaru tsakanin 25 da 57 sun samu raunuka da konewa a sassa daban-daban na jikinsu. An ceto su cikin gaggawa kuma aka garzaya da su asibitoci mafi kusa domin samun kulawar likitoci.
A yayin aikin ceto, an ruwaito cewa wani jariri an jefa shi daga saman bene zuwa ƙasa inda mutane suka yi nasarar kamawa kafin ya faɗi. Hukumar Kashe Gobara ta ƙasa ta yi gargaɗi ga jama’a da su guji irin waɗannan matakai masu haɗari a lokacin gaggawa, domin hakan na iya janyo asarar ray





