Babban Hafsan Sojin Ruwa na Najeriya (CNS), Vice Admiral Emmanuel Ogalla, ya bayyana cewa rundunar sojin ruwa ta samu nasarar murkushe fashin teku da sauran laifukan ruwa a dukkan ruwan Najeriya, wanda hakan ya taimaka wajen ƙara yawan samar da mai da kuma dawo da kwarin gwiwar masu saka jari a harkar ruwa.
Vice Admiral Ogalla ya yi wannan jawabi ne yayin wani biki na “regimental parade” da aka shirya a girmamansa a Makarantar Soja ta Najeriya (NMS), Zariya, inda ya kuma kaddamar da wasu ayyuka tare da yin jawabi ga ɗaliban makarantar da ya fito.
Ya ce tun lokacin da ya hau kujerar shugabanci, rundunar sojin ruwa ta samu gagarumar nasara a harkokin tsaro, inda ya jaddada cewa yankin ruwan Najeriya (EEZ) ya kasance ba tare da an samu wani fashin teku ba tun daga shekarar 2022.
“Tun farko, manufarmu ita ce mu dakile barazanar masu aikata laifukan ruwa. A yau ina alfahari in ce mun cimma wannan buri. Shaida ita ce yadda samar da mai ya ƙaru sosai da kuma bacewar fashin teku baki ɗaya daga ruwanmu,” in ji Ogalla.
Ya danganta nasarorin da aka samu da dabarun rundunar musamman aikin Operation Delta Sanity, wanda aka gudanar tare da haɗin kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a harkar ruwa. Wannan aiki, a cewarsa, ya tarwatsa ƙungiyoyin masu satar danyen mai, masu yin tace mai ba bisa ƙa’ida ba, da sauran miyagun ayyukan ruwa.
Ogalla ya ƙara da cewa waɗannan nasarori sun taimaka wajen ƙarfafa kuɗaɗen shiga na ƙasa tare da mayar da Najeriya matsayin kasa mai tsaro da kuma wuri mai jan hankalin saka jari a harkar ruwa.
Ya jaddada cewa samar da mai ya karu, kudaden shiga na kasa sun haɓaka, sannan amincewar duniya da harkar ruwa ta Najeriya ta dawo. “Yanzu masu saka jari suna kallon Najeriya a matsayin cibiyar ruwa mai aminci da dogaro,” in ji shi.
Shugaban rundunar ya nanata muhimmancin tsaron ruwa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, la’akari da dogaron ƙasar akan man fetur. Ya ce: “Ta hanyar kare ruwanmu, muna kare tattalin arzikimmu kai tsaye. Rundunar sojin ruwa ce garkuwar kare martabar kasa da ikon ta a teku.”
Ya yaba da jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar a dukkan matakai, inda ya yi musu godiya bisa kwazon da suka nuna. Duk da haka, ya gargadi jami’an tsaro da kada su yi sakaci, yana mai cewa masu aikata laifi kan canza dabaru. Don haka ya bukaci ci gaba da horaswa, tattara bayanan leƙen asiri da amfani da sabbin fasahohi.
A kan ziyararsa ta komawa makarantar NMS, Ogalla ya bayyana hakan a matsayin dawowa gida mai cike da tarihi. “Tsayawa a nan yau, ba kawai a matsayin Shugaban Sojin Ruwa ba, amma a matsayin ɗan wannan makaranta, na cika da godiya. NMS ce ta gina halayena, jajircewa da shugabanci,” in ji shi.
A wani bangare na gudummawar sa, Ogalla ya kaddamar da ginin ajujuwa guda shida na zamani da aka samar da kayan koyarwa na fasaha. Ya ce wannan aiki zai taimaka wajen haɓaka kwarewar ɗalibai da kuma shirya su ga kalubalen gaba.
Ya kuma yi alkawarin ƙarfafa haɗin kai tsakanin Makarantar Soja ta Najeriya da makarantar rundunar sojin ruwa da ke Ikot Ntuen, jihar Akwa Ibom, domin zurfafa ilimin soja da ladabi a matasa.
Ogalla ya yaba wa Babban Hafsan Soja, Laftanar Janar O.O. Oluyede, bisa gyaran “Boys’ Lines” da wasu muhimman gine-gine a makarantar. Haka kuma ya jinjinawa kungiyar tsofaffin daliban NMS saboda goyon bayansu wajen ci gaban makarantar.
A nasa jawabin, kwamandan NMS, Birgediya Janar Owoicho Ejiga, ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa ɗalibai da kuma kara wa makarantar martaba.
Vice Admiral Ogalla ya kammala da cewa nasarorin da rundunar sojin ruwa ta samu suna da nasaba kai tsaye da farfadowar tattalin arzikin ƙasar. “Mun murkushe fashin teku. Mun ƙara samar da mai. Kuma da hakan, muna tabbatar da makomar Najeriya,” in ji shi.




