Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kai babbar doka ga masu safarar dabbobi daji ta hanyar haram, bayan kama sassan jakuna da darajarsu ta kai ₦3.94 biliyan, tare da mika su hukuma mai kula da daidaito da dokokin muhalli (NESREA) a Jihar Kaduna.
Wata sanarwa da hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a ta bayyana cewa jami’an Sashen Ayyuka na Tarayya (FOU), Yanki B, Kaduna, ne suka kama kayan bayan wasu shirye-shiryen sintiri da yaƙi da fasa-ƙwauri.
An bayyana cewa abin da aka kama ya haɗa da jakunkuna 700 na ƙasusuwan jaki da darajarsu ta kai ₦1.86 biliyan da kuma fatar jakuna 2,500 da aka busar da darajarsu ta kai ₦2.07 biliyan. Ana shirin fitar da kayan zuwa ƙasashen waje ta haram, abin da ya saɓa wa dokokin Najeriya da kuma yarjejeniyar ƙasa da ƙasa irin su CITES.
An gudanar da bikin mika kayan a ranar Talata a Kaduna, inda Kwamanda Aminu Sule, Kwanturolan FOU Zone B, ya mika su ga Kooodinetan NESREA na jihar, Mista Hene Emmanuel.
Kwamanda Sule ya yi nuni da illolin tattalin arziki da irin wannan safara ke haifarwa, yana mai jaddada cewa jakuna na taka muhimmiyar rawa ga al’ummomin karkara wajen samar da hanyoyin sufuri da kuma abin dogaro na rayuwa. Ya gargadi cewa yawan yanka su ba tare da tsari ba na barazana ga dorewar ci gaban al’umma.
“Wannan kama sakon gargadi ne ga ‘yan fasa-ƙwauri: FOU Zone B ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaƙi da laifukan muhalli,” in ji Sule.
Kooodinetan NESREA na jihar, Hene Emmanuel, ya tabbatar da karɓar kayan, tare da yabawa hukumar kwastam bisa dabarun aikin leken asiri da suka kai ga nasarar kamen.
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a ɗauki matakan shari’a kan waɗanda ake zargi da hannu a wannan laifi, domin dakile buƙatar da ke kara sa jakuna shiga hatsarin bacewa a ƙasar.
Bikin mika kayan, wanda wakilan hukumomin tsaro da na kula da muhalli suka halarta, ya ƙare da mika kayan sassan jakunan ga NESREA domin ɗaukar ƙarin matakai bisa doka ta kare muhalli ta Najeriya.





