Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kaddamar da luguden wuta kan maboyar ’yan bindiga a Kakihun, Oke-Ode, Babanla da sauran yankuna na kusa a Jihar Kwara, bayan mummunan harin da aka kai safiyar Lahadi a garin Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun.
A yayin harin, ’yan bindiga dauke da makamai suka mamaye unguwar Ogbayo da ke Oke-Ode, inda suka bude wuta ba kakkautawa a kan jama’a da ’yan sa-kai. Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu ciki har da Baale (shugaban al’ummar) Ogbayo.
Daraktan Hulda da Jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar a cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa an gudanar da ayyukan bincike da tallafin luguden wuta domin fatattakar barazanar. Ya ce an kai farmaki kan ’yan ta’adda da aka hango gabashin Babanla, yayin da jiragen leken asiri suka tattara muhimman bayanai don taimaka wa dakarun kasa.
“NAF na tabbatar wa ’yan Najeriya da jajircewarta wajen kare iyakokin kasar da kuma kiyaye al’umma daga miyagun mutane. Ana bukatar jama’a su kasance cikin kwarin gwiwa da wayar da kai yayin da rundunar soji ke kara kaimi wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar,” in ji Ejodame.
Sanarwar ta kara da cewa wadannan hare-haren sun taimaka wajen tabbatar da tsaron wuraren soja, da kuma nuna karfin sojin sama, tare da matsa lamba kan ’yan bindiga don hana sake faruwar irin wannan hari.
A gefe guda, lamarin ya tsananta a daren Lahadi lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kan kauyen Marri da ke karamar hukumar Patigi. Maharan sun far wa kauyen tsakanin karfe 9 na dare zuwa 11, a yayin ruwan sama mai tsanani, inda suka kashe mutum daya, suka jikkata wani, sannan suka kwashe babura da dama.
Sai dai majiya ta tsaro ta bayyana cewa Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta amsa kiran gaggawa cikin sauri, inda ta bi sawun ’yan ta’addan har ta kwato dukkan baburan da aka sace. Wannan mataki ya kawo dan sassaucin rai ga mazauna, kodayake fargabar hare-hare na gaba har yanzu na ci gaba a arewacin Kwara.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da hadin gwiwa da soji da Hukumar Tsaron Dajin Kasa wajen bin diddigin maharan domin cafke su.





