Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta yi gaggawar kai dauki sakamakon barkewar gobara a wani gidan zama da ta samo asali daga na’urar lithium solar inverter a Suncity Estate, Galadima, Abuja.
Ayyukan kashe gobarar sun gudana ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT). Tawagar kashe gobarar daga Hedikwatar Tarayya ta RED HOUSE karkashin jagorancin DSF Bolaji, tare da tawagar tashar Apo karkashin DSF Ogwuche, sun isa wurin, yayin da Hukumar Kashe Gobara ta FCT ta mara musu baya wajen shawo kan gobarar.
Bayan samun gaggawar sanarwa daga mazauna yankin, jami’an kashe gobara sun yi nasarar shawo kan gobarar bayan aikin ceto da ya dauki tsawon awa guda. An ceto dukiyoyi da darajarsu ta kai kimanin ₦700 miliyan, kuma babu asarar rai da aka samu.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta gargadi al’umma da su yi taka-tsantsan wajen girkawa, amfani da kuma kula da na’urorin solar inverter. Hukumar ta jaddada cewa dole ne kwararrun masu sana’a ne kawai su rika girka irin wadannan na’urori, a tabbatar da samun isasshen iska a wurin da aka girka su, tare da yin duba akai-akai domin kauce wa dumama da ka iya haddasa gobara.
Hukumar ta sake jaddada muhimmancin kai rahoton gaggawa da wuri, inda ta bayyana cewa sanarwa cikin lokaci na taimakawa wajen rage asara da kuma hana yaduwar gobara.




