Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service – FFS), Olumode Samuel Adeyemi, ya samu karramawar Thomas Sankara Pan-African Prize for Excellence, yayin da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta samu Lambar Yabo da Girmamawa ta Ƙungiya daga Ƙungiyar Matasa ta Pan-Afirka, Youth Partnership for Africa’s Development (YOUPAD).
An gabatar da lambobin yabon ne a lokacin wata ziyara ta girmamawa da shugabannin YOUPAD suka kai wa Babban Daraktan a Hedikwatar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ke Abuja. Wannan karramawa ta nuna muhimmiyar rawar da Hukumar ke takawa wajen ƙarfafa tsarin tsaro da kare rayuka, ta hanyar aikin ceto na gaggawa, rigakafin gobara, da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin ƙasar.
Da yake gabatar da lambobin yabon, Shugaban YOUPAD, Mista Henry Nwankwo, ya yabawa Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya bisa tsari mai kyau da ingantaccen aiki. Ya bayyana cewa Hukumar ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan kiyaye gobara, inganta dabarun rigakafi, da kuma shirya al’umma yadda za su fuskanci lamurran gaggawa. A cewarsa, lambar yabo ta Pan-Afirka da aka bai wa Babban Daraktan na nuna kyakkyawan jagorancinsa da gudunmawarsa ga ci gaban ƙasa.
A nasa jawabin, CGF Adeyemi ya nuna godiya ga YOUPAD bisa wannan girmamawa, tare da yabawa ƙungiyar kan ayyukanta na Pan-Afirka, musamman wajen yaƙi da shaye-shaye da sauran munanan dabi’u a tsakanin matasa. Ya kuma jaddada ƙudirin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya na ci gaba da haɗa kai da sahihan ƙungiyoyi domin tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta tarbiyya, wayar da kai kan tsaro, da ci gaba mai ɗorewa.
YOUPAD ƙungiya ce ta matasan Pan-Afirka wadda ke inganta jagoranci, shiga harkokin jama’a, da sauye-sauyen zamantakewa domin bunƙasa rayuwar matasa da ci gaban Afirka baki ɗaya.



