Shugaban Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN), Farfesa Olufemi Peters, ya kai ziyarar ban girma ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, a Hedikwatar ‘Yan Sanda dake Abuja, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da rundunar ‘yan sanda ta Najeriya.
Tare da wasu daga cikin manyan jami’an gudanarwa na jami’ar, Farfesa Peters ya nuna godiya ga rundunar ‘yan sanda bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa jami’ar, musamman wajen kafa Cibiyar Musamman ta Nazarin ‘Yan Sanda da ke Dei-Dei, Abuja.
Ya sake jaddada kudirin jami’ar NOUN na bai wa ‘yan Najeriya damar samun ilimin gaba da sakandare cikin sauƙi da sassauci, ba tare da la’akari da sana’a, wuri ko jadawalin aiki ba, yana mai bayyana Cibiyar Nazarin ‘Yan Sanda a matsayin shaida ta jajircewar jami’ar wajen wanzar da ilimi ga kowa.
Farfesa Peters ya kuma yaba wa IGP da shugabannin rundunar ‘yan sanda bisa irin haɗin kan da suka nuna wajen cimma wannan buri, tare da kiran a faɗaɗa cibiyar don ta karɓi karin jami’an ‘yan sanda masu sha’awar ci gaba da karatu da bunƙasa sana’arsu.



