Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) ta fara gudanar da cikakken binciken tsaron gobara a fadin kasar nan, bayan kaddamar da Ƙananan Kwamitoci na Musamman a dukkan Kwamandojin Jihohi. Wannan mataki na daga cikin dabarar kasa ta inganta hanyoyin kare afkuwar gobara da kuma tabbatar da bin ka’idojin tsaron gobara a gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.
An gudanar da kaddamarwar ne ta hanyar taron bidiyo, a madadin Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, inda Shugaban Kwamitin Musamman kan Binciken Gine-ginen Jama’a da Masu Zaman Kansu, Mataimakin Babban Darakta (ACG) B. T. Mohammed, ya jagoranci taron. Kaddamar da Ƙananan Kwamitocin na nuni da fara aikin bincike da duba tsaron gobara cikin tsari daya a fadin kasa.
A jawabinsa, ACG Mohammed ya umarci mambobin Ƙananan Kwamitocin da su gudanar da aikinsu cikin cikakkiyar gaskiya, kwarewa, da rikon amana. Ya bayyana aikin binciken a matsayin muhimmin aikin kasa da ke da nufin gano gibin tsaron gobara, tabbatar da bin dokoki, da kuma hana afkuwar gobara da za a iya kauce musu a gine-gine a duk fadin Najeriya.
Ya kara jaddada bukatar jami’an su yi aiki ba tare da tsoro ko son kai ba, tare da bin ka’idoji da dabi’un aikin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya. A cewarsa, sahihan rahotanni, cikakken rubuce-rubuce, da kuma kai rahoto cikin lokaci su ne ginshikan nasarar aikin, wanda zai karfafa shirye-shiryen kare gobara da martanin gaggawa a matakin kasa.
Yayin da yake jawabi ga al’umma, Shugaban Kwamitin ya nemi hadin kai da fahimta daga jama’a, yana mai jaddada cewa aikin binciken ba wai don kawo cikas ga harkokin kasuwanci ko rayuwar yau da kullum ba ne. A maimakon haka, manufarsa ita ce kare rayuka, dukiyoyi, da muhimman kadarorin kasa. Ya bukaci masu gine-gine da mazauna wuraren da su bi ka’idojin tsaron gobara, su aiwatar da gyare-gyaren da aka ba da shawara, tare da kallon aikin a matsayin hadin gwiwa don samar da muhalli mai tsaro ga kowa da kowa.



