Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen intanet da ke zargin cewa wasu sojoji na barazanar tayar da tawaye sakamakon batun albashi da alawus alawus.
A cikin wata sanarwa, Rundunar Sojin ta bayyana rahoton da Sahara Reporters ta wallafa a matsayin karya, mai ruɗani da kuma cike da neman tayar da hankali, wanda aka tsara domin rage amincewar jama’a ga Rundunar Sojin Najeriya da kuma barazana ga tsaron kasa.
Rundunar ta jaddada cewa babu wani lokaci da aka taba samun barazanar tawaye a cikinta. Ta bayyana tawaye a matsayin babban laifi a karkashin dokokin soja, wanda bai dace da akida, ladabi da kwarewar sojojin Najeriya ba. Rundunar ta kara da cewa jami’anta da dakarunta suna biyayya ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da kuma Shugaban Kasa, wanda shi ne Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa.
Sanarwar ta bayyana cewa rahoton ya dogara ne kacokan kan bayanai marasa tabbas daga tushe marasa suna, da aka yada ta hanyoyin da ba na hukuma ba. Rundunar ta ce irin wadannan labarai ba sa wakiltar ra’ayoyi, halaye ko dabi’un jami’anta da dakarunta, wadanda aka horar da su su bi hanyoyin da aka tanada na cikin gida wajen gabatar da koke koke, ba kafafen jama’a ba.
Domin kauce wa rudani, Rundunar ta bayyana cewa karin albashi sakamakon karin mukami bangare ne kawai na jimillar abin da sojoji ke samu, kuma bai kamata a gabatar da shi a matsayin cikakken albashi ba. Albashin soja ya kunshi albashi na dindindin, alawus bisa mukami, alawus na aiki, na fagen daga da na wahala, da sauran hakkoki da ke bambanta gwargwadon inda aka tura soja, kwarewa da nauyin da aka dora masa.
Rundunar Sojin Najeriya, tare da hadin gwiwar Rundunar Sojin Kasa baki daya da sauran hukumomin gwamnati masu alaka, na ci gaba da aiwatar da tsare tsaren inganta jin dadin sojoji. Wadannan sun hada da duba albashi lokaci zuwa lokaci, karin alawus na aiki, ingantaccen masauki, kula da lafiya da kuma shirye shiryen inshora ga sojoji da iyalansu. Batutuwan alawus kuwa na ci gaba da dubawa a karkashin tsare tsaren gwamnati da aka amince da su.
Sanarwar ta kara da cewa Babban Hafsan Sojin Kasa, tun bayan karbar ragamar aiki, ya fara tattaunawa mai amfani da hukumomin da abin ya shafa kan jin dadin sojoji, kuma wannan na haifar da sakamako mai kyau a hankali.
Sabanin ikirarin sakaci, Rundunar ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ta nuna jajircewa wajen kula da jin dadin sojoji da inganta karfinsu na aiki, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen tsaro iri iri.
Rundunar Sojin Najeriya ta sake tabbatar da kanta a matsayin runduna guda daya, mai ladabi da kwarewa, wadda ta mayar da hankali kan aikin kundin tsarin mulki na kare ikon kasar da kuma tallafa wa ayyukan tsaron cikin gida. Ta gargadi cewa kokarin nuna rundunar a matsayin marar tsari ko doka abu ne mara tushe kuma mai illar gaske ga tsaron kasa.
Rundunar ta bukaci jama’a da su yi watsi da irin wadannan rahotanni marasa tushe tare da dogaro da hanyoyin sadarwar hukuma domin samun sahihan bayanai game da Rundunar Sojin Kasa, musamman Rundunar Sojin Najeriya.




