Babban Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Olumode Samuel Adeyemi, ya fitar da kakkausar gargadi ga ’yan Najeriya kan mummunar dabi’ar dibbo man fetur ko dizal daga tankokin dakon mai da suka kife ko suka yi hatsari.
Adeyemi ya bayyana wannan aiki a matsayin sakaci mai hatsari da ke janyo asarar rayuka, yana mai jaddada cewa babu wani adadin mai da ya fi darajar rayuwar dan Adam. Gargadin ya biyo bayan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna mutane suna dibbo mai daga wani tanki da ya kife a gadar Tincan Liverpool a Apapa, jihar Lagos.
Ko da yake daga baya an tabbatar da cewa tankin dizal ne yake dauke da shi, Babban Daraktan ya ce wannan bai rage hatsarin abin ba, domin yadda mutane suka ruga wajen dibbo man ya sake nuna wata tsohuwar dabi’a mai matukar hadari da ta jawo mummunan asarar rayuka da dukiya a sassa daban daban na kasar nan.
Bisa kididdigar hukumomi masu alaka da harkar tsaro, akalla ’yan Najeriya 411 sun rasa rayukansu a shekarar 2024 yayin da suke kokarin dibbo fetur ko dizal daga tankokin da suka yi hatsari. Wannan ya sanya dibbo mai daga tankokin da suka yi hatsari cikin manyan abubuwan da ke haddasa mace mace bayan hadurran mota a fadin kasar.
Jihohi irin su Niger, Jigawa, Enugu, Kogi da Rivers sun sha fama da munanan abubuwa, inda mutane suka ruga wuraren da tankoki suka kife domin dibbo mai, lamarin da ya haifar da gobara da ta kashe mutane da lalata dukiya.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta bayyana cewa irin wadannan abubuwa na bin tsari guda daya, domin man da ya zube na fitar da hayaki mai saurin kamawa da wuta, wanda kan iya tashi daga kananan wuta, zafin injin mota, sigari ko wutar lantarki ta tsaye. Da zarar wuta ta kama, tana yaduwa cikin gaggawa ba tare da iko ba, tana barin mutane da karancin damar tsira tare da gallaza wa jami’an agajin gaggawa.
Haka kuma, hukumar ta yi gargadin cewa tankokin da suka yi hatsari kan kasance cikin yanayi mara tabbas, wanda ke kara yiwuwar fashewa ko tashi da wuta. Taruwar jama’a a wuraren da mai ya zube na kara hatsari da kuma kawo cikas ga ayyukan ceto. Duk da cewa dizal ba ya kamawa da wuta da sauri kamar fetur, hukumomin sun jaddada cewa har yanzu yana iya kamawa da wuta tare da haddasa munanan kone kone, musamman idan hayakinsa ya taru ko ya hadu da zafi.
Babban Daraktan ya sake nanata kiran da yake yi ga ’yan Najeriya da su fifita tsaro fiye da ribar abu. Ya shawarci jama’a da su nisanci wuraren da tankokin mai suka yi hatsari, su gaggauta sanar da hukumomin ceto, su guji taba ko shakar man da ya zube, tare da hana wasu taruwa a irin wadannan wurare.
Adeyemi ya tabbatar da kudirin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya na ci gaba da wayar da kan jama’a, inganta hadin gwiwar hukumomin agaji da kuma karfafa aiki tare tsakanin hukumomi domin rage mutuwar da ake iya kauce mata sakamakon hatsarin tankokin mai a Najeriya.
A yayin gobara ko wasu lamuran gaggawa, an shawarci jama’a da su tuntubi Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta hanyar lambar waya 0803 200 3557 domin samun agajin gaggawa.





