Sojoji na 6 Brigade na Rundunar Sojin Najeriya, a ƙarƙashin Sashen 3 na Operation Whirl Stroke, sun hana wani yunkurin satar mutane kuma sun ceto mutane uku a Jihar Taraba.
Rundunar Sojin ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Umar Muhammad, Jami’in Hulɗa da Jama’a na 6 Brigade, ya fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce an gudanar da aikin ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, bayan samun ingantaccen bayanai daga sojojin da aka tura a garin Jeb Jeb game da ayyukan wasu masu zargin satar mutane a Ƙauyen Sangai, Unguwar Bachama, na Ƙaramar Hukumar Karim Lamido.
Bayan samun bayanan, sojoji sun gaggauta tashi aiki kuma suka bi sawun masu laifi zuwa iyakar Taraba da Plateau. Da ganin sojojin na gabansu, masu garkuwar sun bar wadanda suka sace suka tsere zuwa dazuzzuka.
Rundunar ta tabbatar cewa wadanda aka ceto sune Nimron Umar Ab (shekaru 25), Safaras Ibrahim (shekaru 20), da Habila Yunusa (shekaru 23).
Sanarwar ta ce wadanda aka ceto suna hannun sojoji, suna karɓar kulawa ta likita kuma ana yin rajista da cikakken bayani a kan su. Bayan kammala wannan, za a mayar da su ga iyalansu.
Kwamandan 6 Brigade na Rundunar Sojin Najeriya, Brigadiya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin kan saurin daukar mataki da ƙwarewarsu, sannan ya sake jaddada ƙudurinsu na ci gaba da ayyukan tsaro a fadin Jihar Taraba.
Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro ta hanyar bayar da ingantattun bayanai a kan lokaci, yana mai cewa irin wannan haɗin kai na jama’a yana da matuƙar muhimmanci ga nasarar ayyukan soja da ake gudanarwa.






