Ƙasa da watanni uku da haukarsa kan mukami, Kwamandan Janar na Hukumar Kariya Daga Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service), Olumode Adeyemi Samuel, ya fara aiwatar da muhimman sauye–sauye domin inganta aikin hukumar a faɗin ƙasar. A zaman gudanarwar farko da ya jagoranta bayan nadin sa, ya bayar da umarnin a tattara duk motocin kashe gobara da suka lalace a dukkan yankunan ƙasar, a gyara su, sannan a mayar da su aiki domin tabbatar da ingantaccen martani a lokutan gaggawa.
A bin diddigin wannan umarni—kuma bayan nasarar gyare-gyare na mataki na farko a Yankin Kudu maso Yamma—Hukumar Kariya Daga Gobara ta Tarayya ta kammala mataki na biyu na aikin farfaɗo da motocin a Yankin Arewa ta Tsakiya. A yau, an mika motoci shida da aka kammala gyaransu, ciki har da Rapid Intervention Vehicle ɗaya da Water Tender guda biyu, a Hedikwatar Federal Fire Service da ke Garki, Abuja.
Kwamandan Janar ya yaba wa Afrodezt Global Services Limited kan kammala aikin cikin inganci da lokaci, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu wajen ƙarfafa ikon martani ga gobara a ƙasa. Ya ce irin waɗannan haɗin gwiwa ne ke tabbatar da cewa Najeriya na da kayan aiki da ƙwararrun motocin da za su kare rayuka da dukiyoyi.



