Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula ta Najeriya (NSCDC) na Jihar Jigawa, Kwamanda Muhammad Kabiru Ingawa, ya yi kira ga dukkan jami’ai da ma’aikatan hukumar da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, ladabi, da kwarewa.
Kwamandan ya yi wannan jawabi ne yayin taron Monday Muster Parade da aka gudanar yau, inda ya ja kunnen jami’ai su guji cin hanci, rashawa da duk wani nau’in karbar abin da bai dace ba, yana mai cewa irin wadannan dabi’u suna sabawa ka’idoji da tushen dabi’un hukumar.
Ya kara da cewa kowane jami’i na NSCDC dole ne ya kasance abin koyi wajen nuna gaskiya da aminci ga kasa da al’umma baki daya.
Kwamandan Ingawa ya kuma shawarci jami’ai da ma’aikata su nemi damar yin aiki ko horaswa a wasu jihohi domin fadada kwarewarsu, koyon sababbin dabaru daga wasu, da kuma inganta yadda ake gudanar da aiki yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa irin wannan gogewa za ta taimaka wajen karfafa iya aikin jami’ai da inganta nasarar hukumar wajen cika manufarta ta kare rayuka, dukiyoyi, da muhimman kadarorin kasa.
A karshe, Kwamandan ya bukaci jami’ai da su ci gaba da zama masu kwazo, lura, da sadaukarwa ga manufofin hukumar tare da kiyaye halayya mai kyau a wajen aiki da kuma wajen rayuwar yau da kullum.



