Sabon tashin hankali ya sake girgiza Jihar Kaduna bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Farin Dutse da ke Karamar Hukumar Kauru, inda suka kashe wani fasto na cocin United Church of Christ in Nigeria (UCCN), wanda aka fi sani da HEKAN, tare da sace fiye da mutane 20 da suka zo ibada.
Lamarin ya faru da safiyar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, lokacin da wasu maharan dauke da makamai suka mamaye garin, suna harbe-harbe ba kakkautawa, wanda hakan ya sa mazauna yankin suka tsere cikin dazuka domin tsira da rayukansu. Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da wasu mambobin cocin HEKAN da ke gudanar da ibada a lokacin.
A cikin wata sanarwa da shugaban cocin HEKAN, Fasto Dokta Amos Kiri, ya fitar, ya bayyana harin a matsayin na zalunci, rashin imani, da rashin tausayi, yana mai cewa wannan al’amari wani sabon misali ne na yadda ake ci gaba da zaluntar al’ummomin Kirista a yankin.
Da zuciya mai rauni, muna sanar da duniya cewa an kashe Fasto Yahaya Kambasiya a lokacin harin, kuma wasu mambobinmu da dama sun shiga hannun ‘yan bindiga, in ji Dokta Kiri.
Ya ce bisa rahoton da ya samu daga shugaban majalisar cocin HEKAN na yankin Kauru, Fasto Dauda Gambo, maharan sun iso da asuba suna harbe-harbe. Fasto Kambasiya da wasu suka nemi mafaka a gonar kusa. Da suka zaci maharan sun bar yankin, sai ya fito daga boye, amma aka harbe shi daga baya, harsashin ya ratsa kirjinsa, ya mutu nan take.
Dokta Kiri ya kara da cewa gawar marigayin ta na a dakin ajiye gawa, kuma ana tattaunawa da iyalinsa kan yadda za a gudanar da jana’izarsa.
Ya tuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari kan mambobin HEKAN a yankin ba. A ranar 4 ga Disamba, 2024, ‘yan bindiga sun sace mutum 50 ciki har da wani fasto, Reverend Francis Lawal, wanda daga bisani ya rasu a hannun masu garkuwa da shi. Haka kuma, a ranar 19 ga Oktoba, 2025, an sace mambobi hudu na cocin HEKAN da ke Kakude, har yanzu kuma ba a sako su ba.
Wadannan hare-hare masu maimaituwa sun zama abin damuwa sosai. Muna kira ga jami’an tsaro su dauki mataki cikin gaggawa don ceto wadanda aka sace tare da hukunta wadanda ke da hannu, in ji sanarwar. Iyalai da mambobin da abin ya shafa na cikin mummunar damuwa da tashin hankali.
Fasto Kiri ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu da wadanda ke tsare, yana rokon Allah ya kawo karshen wannan rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kasar. Cocin HEKAN na rokon addu’o’inku ga iyalan marigayin, mambobinmu, da dukkan al’ummar yankin. Muna rokon Allah ya kawo karshen wadannan kashe-kashe da sace-sacen mutane, in ji shi.
Cocin ta ce ta riga ta sanar da Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta Arewa da ta Jihar Kaduna, tare da ofishin ‘yan sanda na Kauru da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki game da lamarin.



