Gwamnatin Jihar Kwara ta karyata rahotannin da ke cewa ’yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi tara a jihar, tana bayyana wannan ikirari a matsayin ƙarya da kuma yaudara ga jama’a.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Hajiya Bolanle Olukoju, ta fitar a ranar Talata, gwamnati ta kuma zargi wasu ’yan adawa, ciki har da Mista Peter Obi, da amfani da dandamalin su wajen yaɗa labaran ƙarya game da halin tsaro a jihar Kwara.
Sanarwar ta ce: “Muna so mu sanar da jama’a cewa wani labari mara tushe na cewa kananan hukumomi tara a Jihar Kwara suna ƙarƙashin mamayar ’yan bindiga yana yawo a kafafen sada zumunta. Wannan ƙarya ce! Babu wani ɓangare na jihar da ke ƙarƙashin ikon ’yan bindiga.”
Hajiya Olukoju ta bayyana cewa duk da cewa akwai wasu matsalolin tsaro a wasu yankuna kaɗan, ba su kai matsayin da za a ce an mamaye jihar ba kamar yadda ake yada ƙaryar.
Ta ƙara da cewa: “Muna da hujjoji masu karfi da ke nuna cewa waɗanda ke yada irin waɗannan labaran ƙarya na goyon bayan miyagu ne, suna nufin su tada hankalin jama’a da kuma raunana kwarin gwiwar al’umma.”
Sanarwar ta kuma nuna takaici ga Mista Peter Obi, inda ta zarge shi da yada wannan labari mara tushe a shafukan sada zumuntar sa.
“Abin takaici ne ganin cewa Mista Peter Obi ya yi amfani da shafukan sa na sada zumunta wajen yada wannan labarin ƙarya. Wannan dabi’a ba ta dace da mutum mai matsayin ɗan kasa nagari ba. Muna roƙonsa da ya goge wannan rubutu domin ba gaskiya ba ne kuma yana iya haifar da tashin hankali,” in ji sanarwar.
Kwamishinar ta roƙi jama’a da su rika tantance gaskiyar bayanai kafin su yada su, tana gargaɗi cewa irin waɗannan labaran ƙarya na iya ƙara damuwa da wahalar da jami’an tsaro wajen gudanar da aikinsu.
“Irin wannan rashin hankali yana ƙara wahalar da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya. Don haka muna kira ga ’yan kasa da su goyi bayan gwamnati ta hanyar ƙin yarda da kuma bayar da rahoton duk wani labarin ƙarya,” sanarwar ta ƙare.





