Masu bindiga sun hallaka wani sanannen likitan dabbobi da ke Abuja, Dokta Ifeanyi Ogbu, tare da sace ‘ya’yansa uku a lokacin harin da suka kai gidansa da ke yankin Kubwa, kusa da hanyar Kubwa–Kaduna, da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa, Dokta Ogbu, wanda shi ne tsohon shugaban ƙungiyar Nigerian Veterinary Medical Association (NVMA), reshen Babban Birnin Tarayya (FCT), an yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa uku a daren Juma’a. Daga bisani, an tsinci gawarsa a gefen hanya.
Wani abokin aikinsa, Andrew Gabriel Ikechukwu, ne ya tabbatar da mutuwarsa ta hanyar wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Dokta Ifeanyi Ogbu, tsohon shugaban NVMA FCT, wanda aka sace tare da ‘ya’yansa uku daga gidansa a Kubwa, Abuja, an samu gawarsa. ‘Ya’yansa kuwa har yanzu ba a sako su ba. Allah ya sa a samu ceto,” in ji Ikechukwu.
Marigayi Dokta Ogbu an bayyana shi a matsayin ƙwararren likitan dabbobi mai jajircewa da kuma mutum mai tausayin iyali. Ya bar mata da ke jinya da sauran ‘yan uwa da abokai da ke cikin alhini.
Abokan aikinsa da abokansa sun bayyana mamaki da bakin cikinsu kan wannan kisa, suna cewa lamarin babban rashi ne ga iyalinsa da kuma fannin likitancin dabbobi baki ɗaya.
Ana ci gaba da ƙoƙarin gano da kuma ceto ‘ya’yansa da aka sace, yayin da rundunar ‘yan sandan FCT ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba tukuna. Ƙoƙarin da aka yi don samun martani daga hukumar ta hanyar kira da sakon WhatsApp ya ci tura.
Wannan harin ya faru ne cikin mako guda kacal bayan mutuwar ɗan jarida na gidan Arise News, Somtochukwu Maduagwu, wanda aka harbe yayin harin fashi a Katampe, wani yankin Abuja, lamarin da ya ƙara tayar da hankali kan ƙaruwa da rashin tsaro a babban birnin ƙasa.




