Kungiyar Tsofaffin Daliban Cibiyar Kasa (AANI) ta taya Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya da daukacin ‘yan Najeriya murnar bikin cikar kasa shekaru 65 da samun ‘yancin kai, tare da yin kira da a kara hadin kai, kishin kasa, da dagewa wajen tabbatar da tsaron kasa.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Talata, AANI ta bayyana shekaru 65 da Najeriya ta yi a matsayin kasa a matsayin lokaci da ya cika da juriya, bambance-bambancen al’adu, da kuma karfin gwiwar al’ummar kasar. Sai dai ta jaddada cewa wannan lokaci ya kuma dace a yi tunani mai zurfi kan kalubalen da kasar ke fuskanta.
Kungiyar ta yabawa jajircewar Sojoji, jami’an tsaro, da sauran hukumomin kare doka a kokarinsu na yaki da ta’addanci, ‘yan bindiga, da sauran barazanar tsaro a fadin kasa. AANI ta bukace su da su kara kaimi, su fito da sabbin dabaru, tare da ci gaba da jajircewa har sai an samu cikakken zaman lafiya a dukkan bangarorin Najeriya.
Haka zalika, AANI ta bukaci matakan gwamnati na kananan hukumomi, jihohi, da tarayya da su fifita kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, tana mai cewa: “Tsaro shi ne tubalin da hadin kai, ci gaba da wadata ke doruwa a kai.”
“Kungiyar AANI ta yi imani cewa ba gwamnati kadai ke da alhakin tsaro ba. Dukkan ‘yan kasa, kungiyoyi, da masu ruwa da tsaki ne ya kamata su hada kai domin tabbatar da tsaro,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kauce wa rarrabuwar kai ta kabilanci, addini, ko siyasa, su rungumi kishin kasa, gaskiya, da sadaukarwa don amfanin kowa.
“A yayin da muke bikin cika shekaru 65, hadin kanmu shi ne karfinmu mafi girma. Idan muka hade kai da zuciya daya, za mu iya doke barazanar da ke kawo mana tarnaki, mu kuma gina makoma mai daraja wadda ta dace da mafarkin iyayen kafa kasa,” in ji AANI.
Sanarwar ta kammala da addu’a ga shugabannin Najeriya da ‘yan kasa baki daya, tana rokon Allah Ya ci gaba da jagorantar kasar, Ya kare ta, Ya kuma albarkace ta da zaman lafiya da ci gaba.





