Kwamandan Rundunar Special Mining Marshals na Hukumar Tsaro ta Fararen Hula da Kare Muhimman Abubuwan Gwamnati (NSCDC), Assistant Commandant of Corps (ACC) John Onoja Attah, tare da jami’ai da dakarunsa, sun taya Murna ga Babban Kwamandan Hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, Ph.D., mni, OFR, a wajen bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 58. ACC Attah ya bayyana Farfesa Audi a matsayin jagora mai canza al’amura, ginshikin tsari, kuma jajirtaccen ɗan kasa wanda rayuwarsa ta sadaukarwa ta kasance abin koyi da girmamawa a fadin Najeriya.
Yayin da yake tunawa da irin jagorancin CG, Attah ya jaddada cewa a cikin shekaru huɗu kacal na mulkin Farfesa Audi, NSCDC ta sauya zuwa hukuma mai ƙarfi, sahihiya kuma mai hangen nesa. Ya yi nuni da daukar sabbin jami’ai, horarwa da sake horar da sama da jami’ai 5,000 a fadin kasa, tare da faɗaɗa sassan musamman da za su yakar matsalolin ƙasa irin su hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, sata mai, ta’addanci da kuma kariya ga muhimman ababen more rayuwa na ƙasa. A cewarsa, waɗannan nasarorin shaida ne na hangen nesa, ƙarfin hali, da kuma jagoranci mai cike da sauye-sauye na Farfesa Audi.
A madadin Special Mining Marshals, ACC Attah ya yi addu’a ga Allah ya kara wa Farfesa Audi lafiya, hikima da ƙarfi, yana jaddada cewa a shekara 58 rayuwarsa ta zama haske ga jami’an NSCDC da ‘yan Najeriya baki ɗaya. “Muna alfahari da kasancewarka a matsayin jagora da malami,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa Special Mining Marshals za su ci gaba da mara baya ga hangen nesa da manufofin CG domin ƙarfafa NSCDC da kare Najeriya.






