Hukumar Tsaro ta Farar Hula (NSCDC) reshen Jihar Sokoto, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda E. A. Ajayi, ta haɗu da miliyoyin ‘yan Najeriya wajen taya Babban Kwamandan hukumar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, murna a zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara 58. Rundunar ta bayyana Farfesa Audi a matsayin jagora mai hangen nesa, wanda zamaninsa ya ƙunshi sauye-sauye, ladabi da hangen gaba, abubuwan da suka sauya tsarin hukumar a matakin ƙasa tare da ƙarfafa ayyukanta a matakin jiha.
Kwamanda Ajayi ya bayyana cewa ƙarƙashin shugabancin Farfesa Audi, NSCDC ta samu gagarumin cigaba a fannin ɗaukar ma’aikata da horarwa, inda fiye da jami’ai 5,000 aka ɗauka a faɗin ƙasar don cike gibin ma’aikata. Ya ce Sokoto Command ta amfana kai tsaye daga wannan ci gaba, tare da ƙarin kayan aiki, motocin sintiri da na’urorin zamani da suka inganta ayyukan filin. Haka kuma, ya nuna yadda Audi ya bai wa walwalar jami’ai muhimmanci ta hanyar hanzarta ƙarin girma, shirye-shiryen horaswa, tsarin inshora da kula da lafiya, abin da ya ƙara ƙaimi da ƙarfin aiki.
A cikin sakon taya murnarsa a madadin dukan jami’an NSCDC na Sokoto, Ajayi ya yi addu’a ga Allah Ya ƙara wa Farfesa Audi lafiya, hikima da ƙarfi don ci gaba da dorewa a kan irin nasarorin da ya kafa. Ya tabbatar da cewa rundunar ta Sokoto na alfahari da jagorancin Audi, wanda ya sake mayar da NSCDC jajirtacciyar hukuma wajen kare muhimman kadarorin ƙasa, yaƙi da masu lalata kayayyaki, da tabbatar da tsaron al’umma a faɗin Najeriya.





