Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Wuta ta Ƙasa (Federal Fire Service), Samuel Adeyemi Olumode, ya taya Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula (NSCDC), Farfesa Ahmed Abubakar Audi, murna a zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara 58. Ya bayyana rayuwar Farfesa Audi a matsayin abin koyi na kishin ƙasa, jagoranci mai sauye-sauye da kuma jajircewa wajen bauta wa ƙasa, yana mai jaddada cewa gudummawarsa wajen tsaron ƙasa na ci gaba da samun yabo da girmamawa daga sauran hukumomin tsaro.
Olumode ya yaba da sauye-sauyen da Farfesa Audi ya gudanar tun bayan da ya hau kujerar jagorancin NSCDC, wanda ya sake fasalin matsayin hukumar a tsarin tsaron ƙasar. Ya jaddada yadda Audi ya jagoranci ƙarfafa ikon hukumar wajen kare muhimman kadarorin ƙasa, ya faɗaɗa ayyukan leken asiri da na aiki, tare da inganta walwala da horar da jami’an hukumar. Waɗannan matakai, a cewarsa, sun dawo da amincewar jama’a tare da sanya hukumar a matsayin muhimmin abokin haɗin gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar.
A sakon taya murnarsa, Shugaban Hukumar Wuta ya yi addu’a ga Farfesa Audi domin Allah Ya ƙara masa lafiya, basira da ƙarfin guiwa don ci gaba da dorewa kan sauye-sauyen da ya fara. Ya kuma nuna fatan cewa wannan sabon shekara a rayuwarsa za ta kawo ƙarin nasarori yayin da yake ci gaba da ja-gorar NSCDC zuwa manyan matakai na bauta wa ƙasa.




