Hukumar Tsaro da Sa-ido kan Kayayyakin Gwamnati (NSCDC) ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa akwai wasu kudade na karin girma da aka rike ko kuma aka karkatar da su, inda ta bayyana zargin a matsayin yunkurin bata sunan shugabancin hukumar. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACC Afolabi Babawale ya fitar, NSCDC ta fayyace cewa Kwamandan Janar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ba shi da hurumin sarrafa kudaden albashi ko na karin girma, domin wadannan ayyuka na karkashin ikon Kwamitin Shugaban Kasa kan Basussuka ne wanda Ofishin Akanta Janar na Tarayya ke jagoranta.
Hukumar ta tuna wa jama’a cewa lokacin da Farfesa Audi ya karbi shugabanci a shekarar 2021, ya tarar da tarin bashin shekaru biyar tun daga 2015, kuma ya yi nasarar tabbatar da biyan wadannan basussuka ga jami’ai sama da 37,000. Dangane da basussukan shekarun 2020 zuwa 2022 kuwa, hukumar ta tabbatar da cewa an riga an amince da su kuma takardun na nan a ofishin Akanta Janar suna jiran fitar da kudade zuwa tsarin IPPIS. Kazalika, kudaden na shekarun 2023 da 2024 suna jiran amincewar shugaban kasa ne, yayin da ake kan aikin tantance kudaden karin girman da aka yi a watan Disamba 2025.
A karshe, Farfesa Audi ya bukaci daukacin jami’an hukumar da su kwantar da hankulansu su kuma yi hakuri yayin da gwamnati ke kokarin kammala fitar da kudaden. Ya kuma shawarci kafafen yada labarai da su rika tantance bayanai kafin wallafawa domin kauce wa raba kan jami’ai ko haifar da rashin fahimta a tsakanin al’umma, tare da jaddada cewa ba zai taba yin kasa a gwiwa ba wajen fafutukar tabbatar da jin dadin ma’aikatan hukumar.



