Rundunar Tsaron Sibil Difens ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Katsina ta sanar da kama mutane takwas da ake zargi da hannu a harin da aka kai wani ofishinta da ke Koraman Nayalli a cikin birnin Katsina.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Buhari Hamisu, ya tabbatar da hakan a ranar Litinin yayin da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Katsina.
Hamisu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, lokacin da wasu bata-gari suka fito domin nuna fushinsu kan wani samame da ya kai ga mutuwar wani da ake zargin dillalin miyagun ƙwayoyi ne, mai suna Uzairu, wanda aka fi sani da ‘Dan’kuda’. A cewarsa, bata-garin, da yawa, sun kutsa cikin ofishin NSCDC da ke Koraman Nayalli a unguwar Sabuwar Unguwa tare da banka masa wuta.
Ya ce a yayin harin, an ƙona babura guda uku da wasu kayayyaki masu muhimmanci mallakin ofishin.
Hamisu ya ƙara da cewa bata-garin, dauke da makamai, sun kuma nufi wasu ofisoshin NSCDC da na rundunar ’yan sanda da ke Filin Kanada, lamarin da ya tayar da hankula.
Sai dai ya ce dakarun martani na musamman daga NSCDC da rundunar ’yan sanda sun shawo kan lamarin cikin gaggawa ta hanyar ƙarfafa tsaro, kuma an dawo da zaman lafiya a yankunan.
Ya kuma bayyana cewa Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, Abbas Moriki, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin harin.
A cewar Hamisu, Moriki ya kai ziyarar duba wurin da abin ya faru kai tsaye, sannan ya kafa kwamitin mutum bakwai domin tabbatar da sahihin bincike.
Ya ƙare da cewa kwamandan ya yi gargaɗi ga duk masu aikata laifuka da masu lalata tattalin arziki da su daina ayyukan ta’addanci, in ba haka ba za su fuskanci hukuncin doka ba tare da sassauci ba.




