Msurshima Apeh, wadda ta tsira daga mummunan harin Yelwata da ya faru a watan Yunin 2025 a Jihar Benue, ta bayyana kaduwar rayuwarta gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda ta shaida yadda ta ga ‘yan ta’adda sun kashe dukkan ‘ya’yanta biyar a gabanta.
Apeh ta yi jawabi ne gaban Kwamitin Ƙananan Hukumomi kan Harkokin Afrika na Majalisar Wakilai, wanda ya gudanar da zaman jin ra’ayi kan matakin Shugaba Donald Trump na mayar da Najeriya cikin jerin Kasashe Masu Ƙwararan Matsaloli saboda zargin cin zarafin addini da har yanzu ke faruwa.
Yayin da take magana daga Jihar Benue ta hanyar bidiyo, Apeh ta bayyana yadda harin ya faru cikin tsananin tashin hankali.
“Da misalin ƙarfe 9 na dare lokacin da muka kwanta, ‘yan ta’adda Fulani suka kawo mana hari a cikin sansanin Yelwata. An kulle mu a ciki, sannan suka fara sare mutane da gatari tare da harbe-harbe,” in ji ta.
Ta ce daga baya maharan suka zuba fetur a kan ginin sannan suka banka masa wuta.
A cewarta, ta tsira ne bayan ta hango wani itace, ta haye, ta ɓuya a bisansa, daga inda ta shaidi yadda aka kashe ‘ya’yanta biyar.
“Na ɗaga idona na ga itace. Na miƙa hannuna na kama reshe na hau sama inda na ɓuya. A ƙasa ‘ya’yana biyar suna kuka, kuma a gabana ‘yan ta’addan suka yanka su,” in ji ta da hawaye.
Apeh ta ce daga nan ta tsere cikin daji, daga baya kuma aka gano ta, aka ceci rayuwarta sannan aka mayar da ita wani sabon sansani.
“Na gudu cikin daji, daga baya masu ceto suka zo suka fitar da ni daga wurin sannan suka kai mu wani sabon sansani,” ta ƙara da cewa.
Harin Yelwata, wanda aka kai a daren watan Yuni 2025, an danganta shi ga wasu makiyaya masu ɗauke da makamai. Yawan waɗanda suka mutu ya haɗa da fararen hula da jami’an tsaro biyar—sojoji biyu, ɗan sanda ɗaya da wasu biyu. An ƙone gidaje da shaguna, tare da hallaka iyalai gaba ɗaya, ciki har da labarin wata iyali guda 15 da aka kashe baki ɗaya.
Shugaba Bola Tinubu ya soke wasu ayyukansa don ya ziyarci Jihar Benue, inda ya gana da shugabanni da masu ruwa da tsaki don nemo mafita, tare da ziyartar wadanda suka jikkata a asibitoci.
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana harin a matsayin barazana ga tsaron ƙasa, inda ya sanar da kama mutane 26 da ake zargi da hannu a kisan. Ya kuma yi alkawarin tura karin jami’ai domin ƙara tsaurara tsaro.
Lamarin ya jawo fushi da suka daga manyan ‘yan siyasa, kungiyoyin addini da na farar hula, waɗanda ke kira da a yi adalci da kuma ɗaukar matakan gaggawa don hana makamantan hare-hare nan gaba.



