Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da cikakken shirin kiwon lafiya kyauta ga mazauna ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina, a wani ɓangare na dabararta ta hanyar ba da tallafi ga jama’a domin ƙarfafa Operation RUWAN KARFE, aikin soji na ci gaba da yaki da ’yan bindiga a yankin.
An gudanar da shirin ne a kwanakin baya, inda mazauna Faskari suka samu amfanin gwaje-gwajen lafiya, wayar da kai kan kiwon lafiya, rarraba magunguna, rabon shabikan sauro, da kuma tura marasa lafiya zuwa manyan asibitoci idan akwai bukatar hakan. Shirin ya ja hankalin jama’a da dama daga Faskari da makotan yankuna, inda masu amfana da dama suka nuna godiya ga wannan gagarumin taimako na Rundunar Soji.
Yayin bude taron, Kwamandan Cibiyar Horar da Sojoji ta Najeriya (NATRAC), Manjo Janar Abubakar Garba Haruna, ya bayyana cewa wannan shiri na nuna fahimtar Rundunar Soji cewa tsaron kasa ya zarce fagen yaki kawai.
Ya ce:
“Tsaro ba ya tsaya ga bindiga da makamai kadai; yana kuma shafar kula da lafiyar ’yan kasa da jin dadinsu. Wannan aiki na nuna jajircewarmu wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban al’ummomin da muke yi wa hidima.”
Ya kara da cewa lafiyar al’umma muhimmin ginshiƙi ne ga cigaban kasa. Ya yabawa jama’ar Faskari bisa goyon bayan da suke bai wa sojojin da ke gudanar da ayyuka a yankin. Ya kuma yi kira garesu da su ci gaba da kallon Rundunar Soji a matsayin abokan gina kasa, ba kawai rundunar yaki ba.
Hakazalika, Hakimin Ƙaramar Hukumar Faskari, Alhaji Aminu Tukur Usman, ya gode wa Rundunar Soji bisa wannan tallafin kiwon lafiya da kuma sadaukarwar sojoji wajen kare rayuka da dukiyoyi. Ya yi addu’ar Allah Ya ba su nasara a ayyukan su na ci gaba.
An gudanar da shirin ne karkashin jagorancin Sashen Hulda da Jama’a na Cibiyar Horar da Sojojin Najeriya, wanda Manjo Godfrey Anebi Abakpa, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, ya jagoranta a ranar 18 ga Nuwamba, 2025.



