NSCDC Ta Kama Mutane 20 Bisa Laifin Ta’addanci, Garkuwa da Mutane, Lalata Kayan Gwamnati da Zamba, Ta Gano Makamai da Alburusai

Rukuni na Musamman na Leken Asiri na Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) ya kama mutane 20 da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci, garkuwa da mutane, lalata muhimman kayan gwamnati, zamba da sauran laifuka a Abuja (FCT), Nasarawa, Benue, Plateau da Jihar Ondo.

A cewar sanarwar, an gudanar da wannan samamen ne bisa umarnin Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, tsakanin watan Oktoba da Nuwamba, 2025, inda aka samu nasarar cafke gungun ’yan ta’adda da masu aikata manyan laifuka.

Kayan da aka kwato sun haɗa da bindigogi AK-47 guda biyu, G3 guda biyu, harsasai sama da 105, mota Toyota Corolla, babura guda hudu, wayoyin hannu, kayan lantarki, tsafi da kuɗi.

Kwamandan rukunin, AS Dandaura, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama, akwai mutum biyu da aka tabbatar da cewa suna da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci da ke da hannu a hare-haren kabilanci a wasu yankuna na jihohin Benue da Plateau. Haka kuma, an kama wasu biyar da ake zargin manyan masu sayen kayayyakin da aka sata, da wasu da ke da hannu a lalata kayan gwamnati, fashi da makami da zamba.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Ibrahim Hudu (mai shekaru 30) da Hassan Ibrahim (mai shekaru 23) waɗanda suka amsa laifin yin garkuwa da mutane da kisa a Jihar Nasarawa. Sun bayyana yadda suka yi garkuwa da suka kashe Mista Obasanjo H. Aku da Mista Muhammadu Yaka duk bayan karɓar kudin fansa. Bincike ya kuma nuna cewa Hassan Ibrahim na da hannu a hare-haren ’yan bindiga a Guma (Benue) da Qua’an-Pan (Plateau).

A Jihar Ondo kuma, NSCDC ta kama wani Iseoluwa Shadrach Omosehin mai shekaru 27 da bindigogin G3 guda biyu. Haka nan a Nasarawa, an kama wasu da ke lalata kayan wutar lantarki da kuma karɓar kudin wuta daga mazauna unguwa ta hanyar zamba.

Kwamandan Dandaura ya ce an kuma kama wasu mutane biyar da ke sayen kayayyakin da aka sata daga ’yan fashi da masu garkuwa da mutane, domin karya tsarin kuɗaɗen su.

Ya jaddada cewa Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Audi, ya kuduri aniyar ci gaba da yaki da masu aikata laifuka da masu lalata arzikin ƙasa, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Ya ce duk wanda aka kama za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike, sannan ya bukaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri domin kawo ƙarshen aikata laifuka a ƙasar nan.

  • Keji Mustapha

    Related Posts

    Police Dismiss Reports of ‘Shoot-on-Sight’ Order, Clarify IGP’s Remarks on Illegal Firearms

    By Tunji Braimoh, Abuja The Nigeria Police Force has refuted reports alleging that the Inspector-General of Police, Kayode Egbetokun, directed officers to shoot individuals found in possession of illegal firearms,…

    PSM Editorial: The Politics of the N2 Billion Smear Campaign Against Mining Marshals

    The controversy surrounding the alleged N2 billion suspicious transactions linked to officers of the Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) Mining Marshals has exposed what many observers consider a…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Police Dismiss Reports of ‘Shoot-on-Sight’ Order, Clarify IGP’s Remarks on Illegal Firearms

    Police Dismiss Reports of ‘Shoot-on-Sight’ Order, Clarify IGP’s Remarks on Illegal Firearms

    PSM Editorial: The Politics of the N2 Billion Smear Campaign Against Mining Marshals

    PSM Editorial: The Politics of the N2 Billion Smear Campaign Against Mining Marshals

    Mining Marshals Petition Reps Speaker, Dismiss Corruption Allegations as Politically Motivated Smear CampaignWriting

    Mining Marshals Petition Reps Speaker, Dismiss Corruption Allegations as Politically Motivated Smear CampaignWriting

    Blood, Power and Billions: Why Violence Continues to Haunt Nigeria’s Transport Union System

    Blood, Power and Billions: Why Violence Continues to Haunt Nigeria’s Transport Union System

    Federal Fire Service Trains 5,300 Army Recruits on Fire Prevention and Emergency Response in Osun

    Federal Fire Service Trains 5,300 Army Recruits on Fire Prevention and Emergency Response in Osun

    NUJ FCT Pledges Support for Police Complaint Response Unit, Strengthens Accountability Monitoring

    NUJ FCT Pledges Support for Police Complaint Response Unit, Strengthens Accountability Monitoring