Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) na Jihar Jigawa, Kwamanda Muhammad Kabiru Ingawa, ya fara jerin ziyarce-ziyarcen ban-girma ga shugabannin wasu hukumomin tsaro a cikin jihar, domin ƙarfafa haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri, da inganta aiki tare wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
A yayin ziyarar, Kwamanda Ingawa ya gana da CC Ahmed Yusuf Lakpene (FSI), Kwamandan Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) na Jihar Jigawa, da T. A. Musa, Kwamandan Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) na Jihar Jigawa.
Kwamanda Ingawa ya yaba da jajircewa da ƙwarewar waɗannan jami’ai wajen gudanar da aikinsu, inda ya jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin hukumomin tsaro domin shawo kan matsalolin tsaro da kuma kare rayuka, dukiya da muhimman kadarorin ƙasa a fadin Jihar Jigawa.
A nasa bangaren, CC Lakpene da Kwamanda Musa sun yaba da irin jagorancin kwazo da Kwamanda Ingawa yake nunawa, tare da tabbatar da aniyar su na ci gaba da aiki kafada da kafada da NSCDC domin cimma burin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
Kwamanda Ingawa ya bayyana cewa wadannan ziyarce-ziyarcen wani bangare ne na yunƙurinsa na ci gaba da ƙarfafa dangantaka mai kyau tsakanin hukumomin tsaro, ƙarfafa tattaunawa da haɗin kai, da kuma yada kyawawan hanyoyin gudanar da aiki domin amfanin jama’ar jihar baki ɗaya.
A karkashin jagorancinsa, NSCDC Jihar Jigawa ta kuduri aniyar ci gaba da bin ƙa’idar aiki cikin ladabi, ƙwarewa, da faɗakarwa, don tabbatar da tsaron jama’a da kuma kare muhimman kadarorin ƙasa a fadin jihar.




