Rundunar Tsaro ta Farar Hula ta Najeriya (NSCDC) reshen Jihar Kano ta ci gaba da jajircewarta wajen yaki da laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa masu bin doka karkashin jagorancin Kwamanda Mohammed Hassan Agalama.
Bisa sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu jami’an NSCDC sun kama mutane biyu daya bisa zargin satar babur a unguwar Sabuwar Jiddah Yan Kusa da kuma wani da ake zargi da cinikin miyagun kwayoyi a Sabon Titin Dorayi dukkansu cikin Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Wanda ake zargi da satar babur mai suna Usman Abdulhamid mai shekaru 19 mazaunin Yandanko Panshekara Kumbotso an kama shi ne bayan ya saci babur daga hannun wani mutum ba tare da izini ba a yankin Sabuwar Jiddah. Lokacin bincike ya amsa cewa yana cikin wata kungiyar masu satar da karbe babura a sassa daban daban na birnin Kano.
A lokacin samamen jami’an NSCDC sun gano babura hudu 4 daga hannunsa uku 3 Jincheng da daya 1 Lifan Kumata. Ana ci gaba da kokarin cafke sauran abokan aikinsa guda biyu da suka tsere.
Haka kuma wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi Salisu Abdullahi mai shekaru 28 dan asalin Semegu Kumbotso an kama shi a Sabon Titin Dorayi dauke da wasu sinadarai masu sa maye da ake zargin yana sayarwa don amfani ta haram.
Abubuwan da aka samu daga hannunsa sun hada da miyagun kwayoyi iri iri da wasu kayayyaki da ke da alaka da safarar su. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a kotu domin fuskantar hukunci.



