Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Abubuwan Gina Kasa ta Najeriya (NSCDC), a karkashin jagorancin kwararren kwamandan ta Jihar Sokoto, CC E.A. Ajayi, ta sake jaddada kudurinta na ci gaba da tabbatar da tsari, kwarewa, da ingantaccen aiki.
Da misalin ƙarfe 08:00 na safe, kwamandan ya isa filin taron hedikwatar hukumar dake Sokoto, inda jami’ai suka tarbe shi cikin girmamawa. Daga nan sai ya duba Quarter Guard, wani tsohon tsarin soja da ke nuna girmamawa, daidaito, da shirye-shiryen jami’ai wajen gudanar da ayyukansu.
Bayan haka, Kwamanda Ajayi ya isa filin taron jami’ai domin gudanar da taron musta na kowane Litinin. An fara da addu’o’i daga Limamin hukumar da kuma Chaplain ɗin, domin neman jagora da kariyar Ubangiji ga hukumar da ma’aikatanta.
A jawabinsa, Kwamandan ya bukaci jami’ai da su ci gaba da bin ƙa’idodin tsabta, isowa da wuri, da kuma jajircewa a aiki. Ya gargadi duk wani ma’aikaci da ke sakaci ko barin wurin aiki ba tare da izini ba, yana mai cewa rashin ladabi da sakaci ba za su samu wuri ba a karkashin jagorancinsa.
“Ba zan lamunci duk wani jami’i da ya kasa yin aikinsa na doka ba. Rashin zuwa aiki ko sakaci manyan laifuka ne, kuma duk wanda aka kama yana aikata hakan zai fuskanci hukunci,” in ji shi.
Kwamandan ya kuma ja hankalin jami’ai su rungumi ƙa’idojin hukumar na gaskiya, faɗakarwa, da ingantaccen aiki, yana tunatar da su muhimmancin rawar da hukumar ke takawa wajen kare rayuka, kiyaye muhimman kayan gwamnati da cibiyoyin kasa, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Haka zalika, Kwamandan ya yi nuni da rawar da hukumar NSCDC ke takawa wajen aiwatar da Manufar Kasa ta Kare Muhimman Abubuwan Gina Kasa ta shekarar 2024 (NPPSI), inda ya bukaci jami’ai su yada wannan ilimi ga sauran abokan aiki domin fahimta mai zurfi.






