Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta tura ma’aikatanta zuwa yankunan majalisar dattawa uku na Jihar Anambra domin lura da yadda ’yan sanda za su gudanar da aikinsu yayin zaben gwamna da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban Hukumar, kuma Koodinetan Ƙasa, DIG Hashimu Argungu (rtd), mni, ya ja kunnen ’yan sanda da aka tura ayyukan zabe su nuna ƙwarewa, adalci da ladabi a yayin gudanar da aikinsu. Ya jaddada cewa dole ne su kare jami’an zabe da kayan zabe, tare da tabbatar da cewa an samar da yanayi mai kyau da zaman lafiya domin ’yan ƙasa su kada kuri’unsu ba tare da tsangwama ba.
Argungu ya yi gargadi cewa duk wani jami’in da ya karya dokokin aikin sa ko ya nuna son kai za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.
Ya bayyana zaben gwamnan Anambra a matsayin jarabawa ce ta farko ga rundunar ’yan sanda yayin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaben 2027.
Shugaban Hukumar ya yaba wa Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Anambra da Kwamishaninta, CP Ikioye Orutugu, fwc, PhD, bisa matakan da suka ɗauka domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe. Ya ce ziyarar da kwamishinan ya kai kwanan nan zuwa dukkanin ofisoshin yankuna da wuraren da ake ɗauka a matsayin masu hatsari ta nuna shirin rundunar wajen tabbatar da gaskiya da zaman lafiya a yayin zabe.
Argungu ya tabbatar da cewa Hukumar PSC za ta karrama jami’ai masu gaskiya da jajircewa yayin zaben, sannan za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Ma’aikatan sa ido na Hukumar PSC za su gudanar da aikinsu daga Awka, babban birnin jihar, da kuma cikin dukkanin yankunan majalisar dattawa uku na Jihar Anambra.




