Jamhuriyar Jama’ar Sin ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tare da gargadin ƙasashen waje da su guji tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na Najeriya, bayan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke nuna yiwuwar amfani da sojoji.
Da take jawabi ga manema labarai a birnin Beijing ranar Talata, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin, Mao Ning, ta sake jaddada matsayin Beijing na adawa da amfani da addini ko kare hakkin ɗan Adam a matsayin hujjar tsoma baki cikin harkokin kasashen da ke da cikakken ‘yanci.
A cewar Mao, “A matsayinta na abokiyar hulɗa ta dabarun ci gaba da Najeriya, Sin na goyon bayan gwamnatin Najeriya wajen jagorantar jama’arta bisa hanyar ci gaban da ta dace da yanayin ƙasarta.”




