Pix: Dr. Dele Alake
Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Ƙasa ta bayyana cewa tura ‘Yan Sanda na Ma’adinai (Mining Marshals) ya zama ɗaya daga cikin muhimman matakai da suka fi tasiri a fannin hakar ma’adinai na ƙasar, wanda ya rage ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba tare da ƙara yawan kuɗaɗen shiga daga wannan fanni.
Yayin da yake jawabi a taron shugabannin yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a Akure, Ministan Raya Ma’adinai, Dr. Dele Alake, ya ce ‘Yan Sanda na Ma’adinai sun kwato fiye da wuraren hakar ma’adinai 90 da aka keɓe ba bisa doka ba tare da gurfanar da sama da mutane 300 a kotu, abin da ya dawo da zaman lafiya da tsari a yankunan hakar ma’adinai da suka kasance cikin tashin hankali a baya.
Ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan sauye-sauye da ake aiwatarwa ƙarƙashin Manufar Sabon Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda manufarta ita ce mayar da Najeriya ƙasa mai cike da halaltattun masana’antu da damar kasuwanci.
“‘Yan Sanda na Ma’adinai sun kawo mana sakamako a zahiri. Ba kawai magana muke yi kan hakar ma’adinai ba bisa doka ba, muna kwato su wuri bayan wuri. Yanzu ƙauyuka sun fi aminci, masu zuba jari na gaskiya sun dawo, kuma kuɗaɗen gwamnati na ƙaruwa,” in ji Ministan.
Ya ƙara da cewa, sakamakon ayyukan Marshals da sauran gyare-gyare ya bayyana a lambobi: kudin shiga daga fannin hakar ma’adinai sun tashi daga ₦8.6 biliyan a 2022 zuwa ₦38 biliyan a 2024, yayin da aka riga aka samu ₦30 biliyan a 2025.
Yankin Kudu maso Yamma shi kaɗai ya bayar da gudunmawar ₦7.2 biliyan, abin da ke nuna muhimmancinsa a matsayin cibiyar hakar ma’adinai ta gaskiya da ci gaban albarkatun ƙasa.
Ministan ya ambaci Segilola Gold Project a Jihar Osun, mafi nasara a fannin hakar zinariya a Najeriya, da kuma ɗaruruwan wuraren hakar da binciken ma’adinai a matsayin hujja na yadda masana’antu ke sake samun amincewar masu zuba jari.
Haka kuma, ya bayyana cewa yanzu doka ta wajabta wa kamfanonin hakar ma’adinai su rattaba hannu kan Yarjejeniyar Cigaban Al’umma (Community Development Agreements – CDA) kafin su fara aiki, domin tabbatar da cewa al’ummomin da ake hakar a yankunansu suna amfana kai tsaye.
“A cikin shekaru biyu kacal, al’ummomi 45 na Kudu maso Yamma sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi na CDA, fiye da ninki biyu na abin da aka cimma cikin shekaru goma sha biyar da suka gabata,” in ji shi.
Yayin da yake kallon gaba, Ministan ya bayyana cewa matakin gaba na sauye-sauyen Renewed Hope zai mayar da hankali kan ƙara ƙima ga albarkatun ma’adinai, kafa masana’antun sarrafa ma’adinai, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zuba jari domin mayar da fannin hakar ma’adinai ginshiƙin samar da ayyukan yi da ci gaba mai ɗorewa.
“Muna alfahari da ci gaban da aka samu, amma muna da ƙuduri mai ƙarfi game da abin da ke gaba,” in ji shi a ƙarshe.






