Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farar Hula (NSCDC) a Jihar Kano sun tabbatar da ƙudirin su na ƙarfafa haɗin gwiwa domin inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Wannan bayani ya fito ne a cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano.
A cewar sanarwar, sabuwar dangantakar haɗin gwiwar ta biyo bayan ziyarar ban girma da Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Bala Bawa Budinga, ya kai hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar. Wannan ziyara ta yi daidai da umarnin Sufeton Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ke ƙarfafa tsarin “hadin kai a harkokin tsaro”.
Kwamanda Budinga ya yaba da kyakkyawar alakar da ke tsakanin hukumomin biyu tare da bayyana shirinsa na ƙara zurfafa haɗin gwiwa. Ya ce ya ga dacewar kai wannan ziyara domin neman ƙarin haɗin kai da kuma nuna godiya ga rundunar ‘yan sanda bisa goyon baya tun lokacin da ya hau karagar mulki.
A nasa bangaren, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da kudirin rundunar wajen ci gaba da musayar bayanan sirri da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa, ci gaba da wannan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro muhimmin abu ne wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamandan Makarantar Sakandare ta ‘Yan Sanda da ke Shanono, CSP Hussaini Hashim, ya jagoranci malamai da ɗaliban makarantar zuwa ziyarar ban girma ga Kwamishinan ‘Yan Sanda domin nuna godiya bisa goyon bayan da rundunar ke bayarwa ga makarantar.




