Shugaban Hukumar Kula da Wuta ta Tarayya (Federal Fire Service) na Jihar Gombe, DCF Suleiman Mohammed Suleiman, ya kai ziyarar jaje da nuna goyon baya ga Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Gombe sakamakon gobarar da ta tashi a wani dakin kwanan ‘yanmata na jami’ar kwanan nan.
A yayin ziyarar, DCF Suleiman ya bayyana tausayinsa ga al’ummar jami’ar bisa wannan mummunan lamari, tare da yabawa da gaggawar da sashen kula da wuta na jami’ar da ma’aikatan ta suka nuna wajen dakile gobarar, wanda hakan ya taimaka wajen rage asara.
Ya mika rahoton binciken gobarar ga Mataimakin Shugaban Jami’ar, tare da ba da shawarwari kan matakan kariya da dabarun kauce wa faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
DCF Suleiman ya kuma tabbatar da shirye-shiryen hukumar wajen ci gaba da hadin kai da jami’ar a bangarorin horaswa kan kariya daga gobara, wayar da kai, da kuma gudanar da binciken hadarin gobara lokaci zuwa lokaci.
Hukumar Kula da Wuta ta Tarayya, Jihar Gombe, tana nan daram wajen kare rayuka da dukiyoyi ta hanyar hana gobara tun kafin ta faru da kuma gaggawar kai dauki idan ta taso a duk fadin jihar.




