Kwamandan Brigade ta 18 kuma Kwamandan Sub-Sector 2 na Operation FANSAN YAMMA, Birigedi Janar Ibrahim Babatunde Gambari, ya yaba wa sojojin da ke karkashin jagorancinsa bisa kwarewa, jajircewa da kuma dabarunsu wajen gudanar da aikin mako guda da suka kai ga fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a yankunan Karamar Hukumar Kontagora, Mariga, Rijau da Rafi na Jihar Niger.
A cewar kwamandan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan a wurare da dama, inda suka halaka da dama daga cikinsu ba tare da an samu asarar rai ko kayan aiki daga bangaren rundunar ba. Ya bukaci sojojin da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da jarumta wajen tinkarar duk wani abu na ta’addanci a duk lokacin da aka lura da motsi a cikin yankin da suke da alhakin tsaro.
Birigedi Janar Gambari ya kuma gode wa sashen sojin sama bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar ta hanyar kai farmaki da tallafin iska wanda ya taimaka wajen halaka ‘yan bindiga da kuma kubutar da fursunoni daga hannun masu garkuwa.
Ya bukaci sojojin da su ci gaba da jajircewa da tsare tsaron yankin domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga mazauna yankin da sauran ‘yan kasa masu bin doka da oda domin su gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
Kwamandan Brigaden ya bayyana godiyarsa ga Babban Kwamandan Rundunar Sojoji ta 1 Division kuma Kwamandan Sector 1 Operation FANSAN YAMMA bisa jagoranci, shawarwari da goyon bayan da yake bai wa Brigade din a dukkan matakai na aikin.
Janar Gambari ya kara tabbatar da aniyarsa na ci gaba da bin ka’idojin aiki da ladabi da ke bambanta Sojojin Najeriya, inda ya ce sojojin za su ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Ya kammala da tabbatar wa GOC da sauran masu ruwa da tsaki cewa Brigade dinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da ‘yan bindiga, ta’addanci da duk wasu nau’ikan laifuka a Jihar Niger da ma sauran sassan kasar baki daya.




