Kwamitin Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta sake jaddada kudurinta na gudanar da tsarin daukar ma’aikata cikin gaskiya, adalci da nagarta ga dukkan ‘yan takarar da ke halartar zabin bana.
Kwamitin ta bayyana cewa, tsarin daukar ma’aikata da ake gudanarwa a cikin Hukumar Civil Defence (NSCDC), Hukumar Gyaran Hali, Hukumar Kula da Gobara, da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa za a gudanar da shi ne bisa ingantaccen tsari da cike da gaskiya da amana.
Kwamitin ta shawarci dukkan masu nema da su rika tuntubar kafofin sadarwar hukuma na CDCFIB kawai domin samun sahihan bayanai, da kuma guje wa fadawa hannun ‘yan damfara da ke amfani da shafukan bogi ko sunan hukuma domin yaudarar jama’a.
Haka kuma, CDCFIB ta gargadi jama’a da su guji hulɗa da mutanen da ba su da izini ko shafukan yanar gizo da ke ikirarin suna da iko ko tasiri wajen aikin daukar ma’aikata. Ta jaddada cewa dukkan matakai na daukar ma’aikata ana gudanar da su ne kai tsaye ta hannun hukumar da wakilan da ta amince da su, ba tare da wani biyan kudi ko cin hanci ba.
A cikin wata sanarwa da Shugabar Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Hajiya Juliet Okeh, ta sanya wa hannu, ta jaddada cewa ‘yan takara su dogara ne kawai ga bayanan da hukumar ta wallafa ta shafukan ta na hukuma da na sada zumunta. Ta kuma shawarci masu neman aiki da su kasance masu haƙuri, hankali da bin doka yayin da aikin ke ci gaba.
Hajiya Okeh ta kara tabbatar da cewa gaskiya, amana da damar daidaito sune ginshiƙan aikin hukumar, tana tabbatarwa cewa kowane mai cancanta zai sami damar da ta dace bisa nagarta kawai.
Kwamitin ya kuma tabbatar da jajircewarsa wajen ci gaba da hidima ga ƙasa da gina ɗan adam, inda ya bayyana cewa aikin daukar ma’aikata na bana na nufin ƙarfafa jami’an tsaro, gyaran hali, wuta da shige da ficen ƙasa domin inganta tsaron jama’a da ingantaccen ayyukan gwamnati.




