SOJOJI SUN HANDE HAREKAR BOKO HARAM A BORNO, SUN YI GIRMAMAWA GA JARUMAN DA SUKA RASA RAYUKA

Sojojin hadin gwiwa na Operation HADIN KAI karkashin 21 Special Armoured Brigade sun yi nasarar dakile yunkurin harin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka shirya a yankin Kashimri, karamar hukumar Bama, jihar Borno, a ranar 17 ga Oktoba, 2025.

A lokacin wannan samame wanda aka kaddamar bisa sahihan bayanan sirri, sojojin sun gano tare da lalata sansanonin Boko Haram da dama a yankin. Wannan mataki ya tarwatsa shirin ‘yan ta’addan na kai hari ga fararen hula da kuma tada hankalin al’umma da tattalin arzikin yankin.

A yayin fafatawar, sojojin sun yi artabu mai tsanani da ‘yan ta’addan, inda suka kashe da dama daga cikinsu, wasu kuma suka ji raunuka daban-daban sannan suka tsere.

Sai dai wannan aikin ya zo da babban asara. Kwamandan 202 Tank Battalion, Laftanar Kanar Aliyu Saidu Paiko, tare da wasu jarumai daga cikin dakarun, sun sadaukar da rayukansu domin kare kasar. Wadannan jarumai sun nuna jarumta da kishin kasa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Najeriya, kuma za a ci gaba da tuna su da girmamawa da godiya.

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, a madadin jami’ai da dakarun Sojojin Najeriya, ya mika ta’aziyya mai zurfi ga iyalan wadanda suka rasu. Ya bayyana cewa wadannan jarumai ba sojoji kawai ba ne, amma iyaye, ‘yan uwa da ‘ya’ya maza da suka nuna jarumta da kishin kasa a lokacin wahala da barazana.

Janar Oluyede ya sake tabbatar da aniyar sojojin Najeriya wajen kawar da dukkanin al’amuran ta’addanci da dawo da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas da kuma fadin kasar baki daya.

A cikin ruhin mutunta jiki da jin kai, rundunar sojojin Najeriya ta roki jama’a da kafafen yada labarai da su guji yada ko wallafa hotunan jaruman da suka rasa rayukansu kafin a sanar da iyalansu. Wannan mataki yana nufin kare mutuncin wadanda suka rasu da kuma kiyaye sirrin iyalansu.

  • Keji Mustapha

    Related Posts

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    Nigeria’s Minister of Defence, General Christopher Gwabin Musa (Rtd), formally assumed duty today, 5 December 2025, at the Ministry of Defence headquarters, Ship House, Abuja. His arrival marked the beginning…

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    Komandan Mining Marshals, John Onoja Attah, ya yi kira ga hukumomin tsaro na Najeriya da su ƙara zurfafa haɗin gwiwa, yana mai lura da cewa kalubalen tsaro da ke sauyawa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    DEFENCE MINISTER MUSA FORMALLY ASSUMES DUTY IN ABUJA

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    KOMANDAN MINING MARSHALS YA KIRA GA ƘARIN HAƘƘOƘIN HADA-KAI TSAKANIN HUKUMOMIN TSARO

    MINING MARSHALS COMMANDER URGES DEEPER SECURITY AGENCY PARTNERSHIP

    MINING MARSHALS COMMANDER URGES DEEPER SECURITY AGENCY PARTNERSHIP

    FFS Kano Command Strengthens Workplace Safety Culture at NDIC Kano

    FFS Kano Command Strengthens Workplace Safety Culture at NDIC Kano

    Commandant Chinedu Revamps Female Squad, Flags Off School Protection Patrols

    Commandant Chinedu Revamps Female Squad, Flags Off School Protection Patrols

    psm