Hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), reshen Jihar Neja, ta musanta rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta kan wani zargin rikici da Mining Marshals dinsu suka shiga a Sabon Daga, karamar hukumar Bosso, a matsayin ba gaskiya ba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, DSC Abubakar Rabiu Muti, ya tabbatar cewa a kimanin karfe 9:22 na safiyar 16 Oktoba 2025, jami’an NSCDC sun fuskanci wasu ‘yan daba yayin da suke kokarin cafke mutanen da ake zargi da aikata haramtattun ayyukan hakar ma’adanai.
Ya bayyana cewa duk da harin, jami’an sun yi hakuri kuma suka janye cikin tsaro, don kauce wa kara tsananta lamarin.
“Muna so mu fayyace cewa babu wani mutum daga cikin fararen hula da ya rasa ransa ko ya jikkata, kuma raunukan da aka samu sun ta’allaka ne kawai ga wasu daga cikin jami’anmu. Duk wani lalacewar da aka ruwaito ya ta’allaka ne ga motocin NSCDC kawai,” in ji Muti.
Ya yi kira ga jama’a da su watsar da rahotannin karya, tare da yabawa ga goyon bayan da suke bai wa hukumar.
“Hukumar za ta ci gaba da kare muhimman kadarorin kasa da ababen more rayuwa,” in ji shi, inda ya tabbatar da cewa za a ba da karin bayani idan bukatar hakan ta taso.





