Sabon Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) na Jihar Jigawa, Kwamanda Muhammad Kabiru Ingawa, ya karɓi bakuncin Hon. Barde Usman Shehu Hadejia, Kwamishinan Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe ta Jama’a (Public Complaints Commission – PCC), wanda ya kai masa ziyarar ban girma a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
A lokacin ziyarar, Kwamishinan ya taya Kwamanda Ingawa murnar sabon nadin sa a matsayin Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, tare da bayyana aniyar hukumar ta PCC wajen ƙarfafa haɗin gwiwa da NSCDC, musamman a fannoni da suka shafi kare haƙƙin jama’a, wayar da kan al’umma, da kuma samar da zaman lafiya ta hanyar sulhu.
A jawabinsa, Kwamanda Ingawa ya gode wa Kwamishinan da tawagarsa bisa wannan ziyara, tare da tabbatar musu da cewa hukumar NSCDC a karkashinsa za ta ci gaba da yin aiki da gaskiya, adalci, da ƙwarewa wajen cika ayyukanta na doka.
Ya kara da cewa haɗin kai tsakanin hukumomin gwamnati yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa, zaman lafiya, da ingantaccen tsarin bayar da ayyuka ga jama’ar Jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya.
Ziyarar ta ƙunshi musayar saƙonnin fatan alheri, tattaunawa kan yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin, da kuma sabunta al





