Kwamandan Hukumar Tsaro ta Jama’a da Kare Muhimman Abubuwa na Ƙasa (NSCDC) reshen Jihar Nasarawa, Kwamanda Brah Samson Umoru, ya kaddamar da jami’ai 300 na Agro Rangers da Commandant’s Crack Squad a babban ofishin hukumar da ke Lafia, babban birnin jihar.
Yayin bikin kaddamarwar, Kwamanda Brah ya bayyana cewa ƙirƙirar waɗannan ƙungiyoyi biyu wani muhimmin mataki ne da aka ɗauka domin ƙarfafa ƙarfin hukumar wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke tasowa a fadin jihar.
Ya ce Agro Rangers za su mai da hankali kan kare manoma, makiyaya, gonaki da dukkan sarkar harkokin noma domin tabbatar da ingantacciyar samar da abinci da zaman lafiya a yankunan karkara, yayin da Crack Squad za ta kasance ƙungiyar gaggawa da za ta mayar da martani cikin sauri kan barazanar tsaro.
Yayin da yake jan hankali ga jami’an da aka kaddamar, Kwamanda Brah ya umurce su da su kasance masu ladabi, ƙwarewa da sadaukarwa wajen aiwatar da aikinsu. Ya ce:
“An zaɓe ku ne cikin kulawa, kuma za ku fuskanci horo mai tsanani domin shirya ku ga aikin da ke gabanku. Ina kira gare ku da ku tabbatar da amincewar da aka ba ku ta hanyar nuna cikakken kishin aiki, haɗin kai, da mutunta haƙƙin ɗan Adam yayin kare rayuka da dukiyoyi.”
Kwamandan ya kuma tabbatar da shirye-shiryen hukumar na yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki a Jihar Nasarawa. Ya bukaci jami’an da su kasance masu himma, tsantseni, da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu, yana mai cewa tsaron jama’a shi ne babban abin da hukumar ke darajawa.
Kaddamar da jami’ai 300 ɗin nan ya zama wani babban ci gaba a kokarin hukumar na ƙarfafa ayyukan tsaron cikin gida da kuma goyon bayan manufofin gwamnati na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaba a Jihar Nasarawa.




