A wani sabon yunƙuri na ƙara inganta tsaron ƙasa da kare lafiyar jama’a, Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Gobara ta Ƙasa (FFS) ya kai ziyarar ban girma ga Babban Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC). Manufar wannan ziyara ita ce zurfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro, ƙarfafa haɗin kai, da inganta dabarun amsa gaggawa a fadin ƙasar.
A yayin taron, shugabannin biyu sun sake jaddada kudurinsu na ci gaba da kare rayuka, dukiyoyi da muhimman kayan aikin ƙasa. Sun jaddada muhimmancin aiki tare tsakanin hukumomin tsaro da na agajin gaggawa wajen fuskantar ƙalubalen gobara, bala’o’i da barazanar da ke iya shafar lafiyar jama’a.
Tattaunawar ta kuma jawo hankali kan bukatar ci gaba da horo, gudanar da hadin gwiwar ayyuka da musayar bayanai a tsakanin hukumomin biyu domin ƙara inganci da saurin amsawa yayin wani lamari na gaggawa.
Ta hanyar ƙarfafa wannan alaƙa, FFS da NSCDC suna kafa kyakkyawan misali na haɗin kai da kishin kasa wajen bauta wa al’umma. Tare, suna da cikakken niyyar tabbatar da Najeriya mai aminci da tsaro ga kowa da kowa.




