Babban Kwamandan Hukumar Kariya Daga Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service – FFS), Olumode Adeyemi Samuel, ya kara wa jami’ai da ma’aikatan hukumar karfin gwiwa yayin wata ziyarar aiki ta musamman da ya kai a tashoshin Kubwa Abuja Metropolitan da Wuse Command a birnin Abuja.
An bayyana wannan ziyara a matsayin ta farko irin ta a tarihin hukumar, wadda ta bai wa Babban Kwamandan damar yin magana kai tsaye da jami’ai, duba yanayin wurin aikinsu, da kuma binciken kayayyakin aiki domin gano inda ake bukatar gyara da kuma kara inganta aikin hukumar.
A jawabin sa, CG Olumode ya tabbatar da kudurinsa na inganta jin dadin jami’an hukumar, yana jaddada cewa su ne ginshikin babban aikinsu na ceton rayuka da dukiyoyi. Ya bayyana shirin kafa cikakkiyar inshora ga jami’ai, bayar da lambobin yabo bisa kwarewa, da kuma samar da lamuni don tallafa musu wajen biyan bukatu na gaggawa.
Haka kuma ya yi alkawarin samar da yanayin aiki mafi dacewa, tare da gargadin jami’ai da su guji shiga harkar cin hanci wajen daukar aiki, su kuma kiyaye ladabi da da’a; inda ya ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Yayin da yake kallon gaba, Babban Kwamandan ya bayyana cewa ana shirin shigar da darasin kare kai daga gobara da ceto mutane a cikin manhajar makarantu, domin wayar da kai da kuma gina sabuwar al’umma mai kula da tsaro da lafiyar jama’a.
Ziyarar ta kare cikin farin ciki, yayin da jami’ai da ma’aikata na Abuja Commands suka nuna godiya da farin ciki da wannan ziyara, suna bayyana ta a matsayin abin karfafa gwiwa da kuma shaida ta sabuwar manufa ta gyare-gyare, inganta walwala, da tabbatar da nagartar aiki a Hukumar Kariya Daga Gobara ta Tarayya.





