Hedikwatar Aikin Gaggawa ta Rundunar Sojojin Ruwa (FOB) da ke Escravos ta lalata wuraren tace mai na haramtacciya guda shida a Ƙaramar Hukumar Warri South, Jihar Delta.
Kwamandan FOB Escravos, Kanal na Ruwa Ikenna Okoloagu, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a garin Warri.
Ya ce an gudanar da wannan samame ne tsakanin 3 zuwa 24 ga Satumba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka kai ga gano wuraren a ƙauyen Obodo Omadino.
A cewarsa, wannan aiki na cikin Operation Delta Sanity II wanda ya yi daidai da umarnin Babban Hafsan Sojojin Ruwa na ƙasa, Vice Admiral Ikechukwu Ogalla, na kawar da ayyukan haramtattu a cikin tekunan Najeriya.
Okoloagu ya bayyana cewa an kama kusan lita 11,550 na danyen mai da aka sace, waɗanda aka adana a ramuka 52 da kuma jaka na roba guda bakwai.
Ya ƙara da cewa an kuma kwace na’urar fumpi guda ɗaya da tsawon bututu (hose) mai aƙalla yadi 22 daga wuraren.





