Hukumar Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) ta bayyana matukar bakin ciki da girgiza bisa rasuwar tsohon Shugabanta, DIG Parry Osayande (ritaya), tana bayyana shi a matsayin gogaggen jami’in ‘yan sanda mai ilimi da bajinta wanda ya bambanta kansa a aikin yi da shugabanci.
Osayande, wanda ya gaji Cif Simon Okeke, wanda shi ne farkon Shugaban Hukumar, an nada shi a watan Afrilu, 2008, daga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. A zamanin jagorancinsa, hukumar ta samu ci gaba mai yawa ciki har da amincewar shugaban kasa wajen gina hedkwatar hukumar, wacce yanzu take tsaye a unguwar Jabi a Abuja.
Ana yawan yabawa Osayande da jarumta, hangen nesa, da kuma karfin shugabanci, wanda ya baiwa hukumar gagarumar nasara a shekarun farko na kafuwarta.
Yayin da yake mayar da martani kan labarin, Shugaban Hukumar na yanzu, DIG Hashimu Argungu, ya bayyana mutuwar Osayande a matsayin babban rashi ga hukumar PSC da kasa baki daya. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa hukumar addu’a, yana mai cewa abin na da matukar ciwo ganin cewa an rasa shugabanni biyu na hukumar a cikin kasa da wata daya.
DIG Parry Osayande ya rasu ne da safiyar Lahadi a garin Benin, Jihar Edo.





