Ministan Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya karrama sabbin Mataimakan Babban Kwamandan (DCG) guda uku na Hukumar Tsaro da Kare Muhimman Abubuwa ta Kasa (NSCDC), inda ya jaddada musu muhimmancin shugabanci na gaskiya, ladabi, da sabuwar jajircewa ga tsaron kasa.
A yayin bikin, Ministan ya bayyana cewa daukakar mukaman ta fito ne bisa cancanta, shekaru a aiki, da adalci, yana mai cewa wannan karin matsayi na nuni da nauyin sabis da sadaukarwa ga ‘yan Najeriya.
“Ba wai sabon alamar mukami kawai kuke sanya ba, ku na ɗaukar sabbin alhakai ne,” in ji shi. “Ku shugabanci da misali, ku rika koya wa wadanda ke biyowa bayanku, ku kuma nuna shugabanci na aminci, tausayi, da jarumta. Dole ne ‘yan kasa su ji tasirin aikin ku ta hanyar tsaro, kare rayuka, da kiyaye muhimman kadarorin kasa.”
Ya kuma tabbatar musu da goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen jin dadin su, ci gaba da gyare-gyare, da kawo karshen tsaikon mukamai a hukumar, yana mai cewa nasarar hukumar na da alaka kai tsaye da samun al’umma masu aminci a fadin kasar.
A cikin sakon sa na fatan alheri, Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya taya sabbin DCG din murna tare da bukatar su tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar kara dagewa wajen aiwatar da aikin hukumar. “Wannan karin girma ba na ku kadai bane; na miliyoyin ‘yan Najeriya ne da ke dogaro da hukumar don tsaro da fata,” in ji shi.
Wadanda aka karrama da matsayin Mataimakan Babban Kwamandan sun hada da: DCG Abdulkadir Sulu, DCG Abiakam-Omanu Christiana, da DCG Bridget Taylor.





