An karrama Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Nasarawa, Kwamanda Brah Samson Umoru, da lambar yabo ta Jagoranci na Kwarai da Kyakkyawan Gudanar da Tsaro daga People Security Monitor.
An bayar da lambar yabon ne domin girmama nagartaccen jagorancinsa, dabarun tsaro na zamani da kuma jajircewarsa wajen kare rayuka da muhimman kadarorin kasa a fadin Jihar Nasarawa.
Tun bayan karbar ragamar jagoranci, rundunar NSCDC ta Jihar Nasarawa karkashin Kwamanda Umoru ta samu gagarumin ci gaba a fannin kwarewa, ingancin aiki, hulda da al’umma da kuma karuwar amincewar jama’a ga Hukumar.
Yayin mika lambar yabon, Babban Daraktan People Security Monitor, Mista Isiaka Mustapha, ya yabawa Kwamanda Umoru bisa sake fasalta harkar tsaro ta hanyar dabaru masu sa ido gaba, ayyuka bisa bayanan leken asiri da kuma kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin hukumomi. Ya bayyana cewa wadannan kokari sun taimaka wajen kara zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a jihar.
A jawabinsa na karbar lambar yabo, Kwamanda Brah Samson Umoru ya sadaukar da lambar yabon ga Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai hangen nesa wanda goyon bayansa ke karfafa samun nasarori a fadin Hukumar.
Haka kuma, Kwamandan ya yabawa jami’ai da dakarun NSCDC na Jihar Nasarawa bisa jajircewa, ladabi da aiki tare, wanda ya ce su ne ginshikin nasarorin da aka samu.
Ya sake tabbatar da kudirinsa na ci gaba da riko da kwarewa, tsaro mai mayar da hankali kan al’umma da kuma kare muhimman kayayyakin more rayuwa, daidai da dokar da ta kafa Hukumar NSCDC.
Wannan karramawa ta kara haskaka martabar Kwamanda Umoru a matsayin shugaba mai sakamako da kuma jagora mai sauyi a cikin Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya.




