Ma’aikatar Tsaro ta sake jaddada ƙudurin ta na ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) domin bunƙasa tsaron ƙasa da inganta daidaitaccen martani ga sabbin barazanar tsaro a faɗin ƙasar.
Wannan ya biyo bayan wata muhimmiyar ganawa da aka yi tsakanin Ministan Tsaro da Babban Kwamandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, OFR, a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Ship House, Abuja.
A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun tattauna dabaru masu amfani da sabbin hanyoyi da za su ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi tsakanin ma’aikatar da NSCDC, tare da mayar da hankali kan ƙarfafa ƙarfin tsaro da bunƙasa tsarin kare ƙasa.
Tattaunawar ta kuma ta shafi inganta aikin tsaro ta hanyar kyakkyawan haɗin kai, musayar bayanan sirri da ayyukan haɗin gwiwa wajen fuskantar nau’o’in rashin tsaro da ke barazana ga ƙasar.
Ganawar ta nuna aniyar ɓangarorin biyu na ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da tsarin tsaro mai ƙarfi, nagari da amsa bukatun jama’a a Najeriya.





