Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), Reshen Jihar Edo, ta tura jami’ai da ma’aikata 1,200 a fadin mazabun sanatoci uku na jihar domin tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Kwamandan NSCDC na Jihar Edo, Kwamanda Akintayo Saidi Ayinla, ya bayyana hakan yayin ganawa da ‘yan jarida a Benin City, inda ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen hukumar na gaba-gaba don kare rayuka, dukiyoyi da muhimman kadarorin kasa a lokacin bukukuwa.
A cewarsa, ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Command, SC Ogbebor Efosa, jami’an da aka tura sun fito ne daga sassa daban-daban na dabaru da ayyukan hukumar, ciki har da sashen yaki da ta’addanci, sashen hana barna, rundunar mata, Agro-Rangers, tawagar sa ido da bibiyar Kwamanda, da kuma Mining Marshals, da sauransu.
Ya bayyana cewa an baza jami’an a wurare masu muhimmanci a fadin jihar, ciki har da wuraren ibada da filayen addu’a, cibiyoyin bukukuwa da nishadi, manyan hanyoyi, kasuwanni, da sauran wurare masu rauni, domin hana aikata laifuka da kuma tabbatar da lafiyar jama’a.
NSCDC ta Jihar Edo ta tabbatar wa mazauna jihar kudirinta na samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali, wanda zai bai wa ‘yan kasa da baki damar yin bukukuwa ba tare da fargaba ba. Kwamandan ya gargadi masu aikata laifuka da su nisanci jihar, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki kan duk wanda ya karya doka.
Ya kuma shawarci jama’a da su kasance masu bin doka da oda, su kuma kasance masu lura, tare da bayar da sahihin bayani a kan lokaci ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen hana aikata laifuka da saurin daukar mataki.
Yayin da yake taya Kiristoci murnar Kirsimeti, NSCDC ta Jihar Edo ta kuma mika sakon fatan alheri ga daukacin mazauna jihar na samun Sabuwar Shekara mai cike da zaman lafiya da albarka.


